05
Feb
Daga KABIRU YUSUF FAGGE Bayan da na saurari bayanan wasu alƙalan gasannin rubuce-rubucen ƙagaggun labarai a mabambantan gasanni, na tsinkayi akwai abubuwan da za su amfani marubuta masu sha’awar shiga gasa don yin nasara. ɗabi’ar karatu Wannan a bayyane yake cewa, yanzu al’umma sun fi son su kalla ko su saurara fiye da karantawa. Idan haka ne, to kai marubuci kana da gagarumin ƙalubale rubuta labarin da zai sa alƙalan gasa ko suna so ko ba sa so za su karanta, wato ko ba don aikin da aka ba su na karanta labarin su yi alƙalanci ba, ko don salo…
