Adabi

Marubuta a dinga bincike kafin rubutu – Gimbiya Rahma

Marubuta a dinga bincike kafin rubutu – Gimbiya Rahma

"Tun Ina firamare na fara rubutu" Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano Sanannen abu ne, rubutun adabi ya ta shi daga hannun masu buga littafai zuwa yanar gizo, wanda hakan ne ya ba wa matasa damar baje basirarsu ba tare da tunanin fara neman kuɗin buga littafi ba. Ta dalilin hakan ya sa ake samun marubuta da yawa masu rubutu kuma mai ma'ana, hakan ya tabbatar da cewa, matasan marubuta na matuƙar ƙoƙari wurin samar da labarai da za su ƙayatar da masu karatu. Duk da cewa, an yi ammana rubutun intanet ba karɓe wa marubuta kasuwa ya yi ba, samar…
Read More
Tarihin Gobir da yadda Gobirawa suka riski Ƙasar Hausa

Tarihin Gobir da yadda Gobirawa suka riski Ƙasar Hausa

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ƙasar Gobir na ɗaya daga cikin ƙasashen Hausa na ainii, an ce ita ɗin tsohuwar daula ce kuma wata babbar ƙasa ce da ta yi iyaka da Agades daga arewa, ta yi iyaka da Zamfara daga Kudu, ta yi iyaka da Mayali daga Gabas, sannan kuma daga yamma ta yi iyaka da Konni. Amma magana anan ita ce, asalinsu ba hausawa bane tunda wasu na cewa asali wai daga gabas ta tsakiya suka fito musamman ma Misira, inda ake da yaƙinin cewa Sarakuna ukku daga cikin sarakunan Misira gobirawa ne. Sarkin Gobir Mai Martaba Alhaji Abdulhamid…
Read More
Na fi gane na buga littafi maimakon na saka a onlayin – R.A. Adam

Na fi gane na buga littafi maimakon na saka a onlayin – R.A. Adam

"Masu hali ba sa ƙarfafa gwiwar marubuta" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU  Rufa'i Abubakar Adam, wanda aka fi sani da R.A. Adamu, wani matashin marubuci ne da ya taso cikin sha'awar karance-karance da rubuce-rubuce har kafin Allah ya sa ya zama mai aikin ɗab'i da zane-zane a na'urar kwamfuta. Yana daga cikin matasan marubutan da suka kafa ƙungiyar Gamayyar Marubutan Jihar Gombe (GAMJIG), domin haɗa kan marubutan Gombe da samar da wasu hanyoyi na bunƙasa cigaban adabi da harshen Hausa. Gwagwarmayar da ya sha a baya a yayin ƙoƙarinsa na ganin ya zama marubuci ya silar kawo sauyi a Jihar Gombe,…
Read More
Gobe za a ƙaddamar da littafin ‘100+ questions before Nikkah’

Gobe za a ƙaddamar da littafin ‘100+ questions before Nikkah’

Daga AISHA ASAS Shahararriya kuma ƙwararriyar mai bayar da shawarwari kan zamantakewar aure da kuma rayuwa bakiɗaya, Khadija Ibrahim, marubuciya da ta jima tana gyara al'umma da alƙalaminta, ta shirya tsaf don bayar da ƙarin gudunmawa ga masu shirin yin aure, wato littafin da zai amsa tambayoyi ɗari har da ɗori da mata da maza suke buƙatar sani kafin su shige daga ciki. Littafin mai suna tambayoyi ɗari da ɗori kafin aure, wanda zai kasance a turance, wato '100+ questions before Nikkah' zai amsa kusan dukkan tambayoyin da ake buƙatar sani game da aure, waɗanda za su fitar da samari…
Read More
Karamcin marubuta ne ya sa na zama marubuciya – Fadila Lamiɗo

Karamcin marubuta ne ya sa na zama marubuciya – Fadila Lamiɗo

"Ba ƙaramar asara masu satar fasaha ke jawo wa marubuta ba" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubutan Jihar Kaduna kamar na sauran jihohi na ba da gagarumar gudunmawa ga cigaban harkokin adabi. Kama daga matakin ƙungiyoyi har zuwa a ɗaiɗaiku, Jihar Kaduna ta kasance sahun gaba wajen ƙyanƙyashe jajirtattun marubuta, masu ƙwazo da basira wajen ƙirƙirar labarai da ayyukan adabi iri daban daban. Fadila Lamiɗo, ɗaya ce daga cikin irin waɗannan marubuta masu ƙwazo da himma, kuma tun fara rubutun ta a shekarar 2016 ta samu karɓuwa da shahara cikin lokaci ƙanƙani. Ta kasance daga cikin matasan marubuta na onlayin da…
Read More
Tarihin juyin mulkin soja na farko a Nijeriya

Tarihin juyin mulkin soja na farko a Nijeriya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Daga ranar 15 zuwa 16 ga watan Janairun shekarar 1966, wasu ƙananan hafsoshin soja masu muƙaman manjo sun aiwatar da juyin mulkin soja na farko wanda suka fara kitsawa tun a watan Agustar shekarar 1965. Waɗannan ƙananan hafsoshin soja, sun yi ikirarin cewa sun shirya juyin mulkin ne a saboda a cewarsu, shugabannin da ke jagorancin ƙasar sun nuna zarmiya, inda suka ce ministocin gwamnati suna sace kuɗaɗen baitul-mali domin amfaninsu. Sai dai kuma a wani ɓangare, akwai masu ikirarin cewa wannan juyin mulki na ƙabilanci ne a saboda daga cikin sojoji 8 da suka ƙulla…
Read More
Matasan marubuta ba sa son ana musu gyara – Mukhtar Ƙwalisa

Matasan marubuta ba sa son ana musu gyara – Mukhtar Ƙwalisa

"A rubutu na yi aure, na yi muhalli na kaina" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ga duk wani tsohon makarancin littattafan Hausa, musamman littattafan labaran yaƙe-yaƙe da na barkwanci ba zai kasa sanin littattafan marubuci Mukhtar Ƙwalisa ba, wanda ya yi suna wajen tsara labarai masu ɗaukar hankali da sanya nishaɗi a zuciyar mai karatu. A wannan makon, shafin Adabi ya gayyato muku ɗan ƙwalisar marubuta, don jin abin da ya sa har yanzu yake ci gaba da wallafa littattafai duk kuwa da kasancewar takwarorinsa da dama yanzu harkar ta gagare su. A tattaunawar da suka yi da wakilin Blueprint Manhaja,…
Read More
Tarihin yaƙin duniya na biyu

Tarihin yaƙin duniya na biyu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Yaƙin duniya na biyu da a Turanci ake kira ‘World War II’ a kan kintse rubutun kamar haka ‘WWII’ ko ‘WW2’, kuma a kan kira shi da Turanci ‘Second World War’. Yaqin dai wani yaqi ne da duniya baki ɗaya suka afka a ciki, wanda ya kwashi tsawon shekaru shida ana gwabzawa, tun daga shekarar 1939 har zuwa shekara ta 1945. Mafi yawan ƙasashen duniya tare da ƙasashe masu qarfi su ne suka ja daga a tsakaninsu, inda suke yaƙan juna. Hakane ya haifar da gagarumin gumurzu tsakaninsu wanda aƙalla mutane sama da miliyan ɗari ne…
Read More
Har yanzu akwai tsofaffin marubutan da ba su yarda da rubutun onlayin ba – Jamila R/Lemo

Har yanzu akwai tsofaffin marubutan da ba su yarda da rubutun onlayin ba – Jamila R/Lemo

"Na samu kaina a harkar rubutu tun Ina 'yar shekara tara" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Ga duk mutumin da ya kasance tsohon makarancin littattafan Hausa ne, musamman littattafan da jajirtattun mata gwanayen riqe alqalami suka wallafa a shekarun baya, ba zai kasa karanta littafin Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ba, marubuciyar 'Mamaya', 'Zaƙi Da Maɗaci', da Bakin Ganga. Wacce bayan kasancewarta marubuciya har wa yau kuma ma'aikaciya ce ƴar jarida, da ta daɗe tana bayar da gudunmawa a harkar ilimi da cigaban al'umma. Littafinta na 'Kanya Ta Nuna' da ta fara bugawa a shekarar 2002 ya kasance zakaran gwajin dafi, wanda…
Read More
Tarihin yaƙin duniya na farko

Tarihin yaƙin duniya na farko

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A tarihi, yaƙin duniya na ɗaya wanda a Turance ake kira da ‘World War I’ ko ‘First World War’ wani yaqi ne wanda manyan ƙasashen duniya, musamman na nahiyar Turai (Europe) irin su Ingila (Britain), France, Germany, Russia, Austria-Hungary, Russia, Daular Ottoman ta Turkiya (Ottoman Empire), da kuma Amurka suka fafata, a tsakanin shekarun 1914 zuwa 1919. A bisa tarihi, ya tabbata cewa zuwa shekarar 1900 wato farkon ƙarni na 21, ƙasashen yammacin Turai irin su Ingila, France, Germany, Spain, Portugal, Netherlands, da kuma Italy sun kai ga cikakken ci gaban tattalin arziki (economic development) da…
Read More