Adabi

Gudunmawar sarakunan Nijar wajen bunƙasa al’adu da zaman lafiya

Gudunmawar sarakunan Nijar wajen bunƙasa al’adu da zaman lafiya

Daga WAKILINMU Babu shakka masarautun ƙasar Nijar kaffatanninsu masarautu ne masu cike da haiba da kuma ɗimbin tarihi kuma masu adalci ga al'ummar da suke shugabanta. Duk mutumin da ya kasance mai bibiyar tarihi zai yarda kuma har ma ya aminta cewa sarakunan ƙasar Nijar ba su da kyashi ko baiken jin cewa sun taimake ka wajen samar da tarihi da kuma labarin da abin da ya shafe su, kamar yadda na zama ganau ba jiyau ba kamar yadda hausawa ke azancin magana da cewa wai ‘Gani Ya Kori Ji’. Bari na fara da Masarautar Sultan ta Damagaran a shekarar…
Read More
Sharhin wasu baituka na waƙar Ali Makaho mai taken ‘Fahimta’

Sharhin wasu baituka na waƙar Ali Makaho mai taken ‘Fahimta’

Daga BAMAI A. DABUWA KKM Shimfiɗa: Idan ana maganar rubutu ko waƙa ko kuma aka ce maka Adabi a cure, to ba su da iyaka. Kuma komai daidai ne a harkar. Adabi shi ne madubin rayuwar ɗan Adam. Wato ana kallon rayuwar mutum ne da abin da ke kewaye da shi a rubuta ko a rera shi. Ke nan, kamar yadda yake a zahiri mutane suna sata, caca da sauran laifuka, a Adabi ba zunubi ba ne don ka yi ashariya. A sauƙaƙe, idan akwai wasu mutane da aka yi wa uzurin, ƙarya, batsa da saura to marubuta ne da…
Read More
William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

William Tubman: Wanda ya zamanartar da Laberiya

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Laberiya kasa ce ta 'yantattun bayi, wadda aka gina da musguna wa 'yan ƙasar lokacin da aka zavi William Tubman a matsayin shugaban ƙasa. Bayan haɗa kan mutane, ya shirya ƙasar bisa tsarin ci-gaba wanda bai samu ba. An haifi William Vacanarat Shadrach Tubman ranar 29 ga watan Nuwamba 1895. Ya fito daga yankin kudu maso gabashin Laberiya, daga garin da ake kira Harper na gundumar Maryland. Sunan wuraren ya yi kama da na Amurka, saboda Jamhuriyar Laberiya ta ayyana samun 'yanci daga Amirka a shekarar 1947 da 'yantattun bayi suka yi, waɗanda suka dawo daga…
Read More
Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Ahmed Baba: Shahararren malamin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ahmed Baba ya kasance ɗaya daga cikin manyan malamai na Afirka a ƙarni na 16. Marubuci kana masanin addinin Islama, ya yi aiki game da shari'a kan batun bauta da rubuta tarihin mashahuren mutane. Lokacin da Ahmed Baba ya rayu: An haifi Ahmed Baba a shekarar 1556. Wasu majiyoyi sun ce a Araouane, kimanin kilomita 250 Arewa maso Yammacin Timbuktu, birnin da ke arewacin Mali. Akwai kuma yiwuwar an haife shi a Timbuktu lokacin birnin na bunƙasa a matsayin cibiyar binciken addinin Islama da harkokin kasuwanci na yankin Sahara. Baba ya yi karatu a birnin Timbuktu…
Read More
Ingantaccen rubutu shi ke kai marubuci ko’ina a duniya – Rahmatu Lawan

Ingantaccen rubutu shi ke kai marubuci ko’ina a duniya – Rahmatu Lawan

"Manhajar Hikaya ba ta ɗora littattafan batsa" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Masu bibiyar wannan shafi na Adabi muna yi muku fatan alheri a kodayaushe. Kamar kowanne mako, yau muna ɗauke ne da wata tattaunawa da muka yi da Hajiya Rahmatu Lawan Ɗalha, wata ƙwararriya a harkar sarrafa fasahar sadarwa wacce ita da mijinta masanin fasahar zamani suka samar da Bakandamiya Hikaya, wasu tagwayen manhajoji da ke ba da gudunmawa ga cigaban rubutun adabi da rayuwar marubuta. Ɗaya manhaja ce ta ƙarfafa zumunci tsakanin marubuta da masu karatun littattafansu, sai kuma manhajar tallata littattafai da rubuce-rubuce na ilimi. A tattaunawar da…
Read More
Asalin Birnin Timbuktu

Asalin Birnin Timbuktu

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Tombouctou ko kuma Timbuktu, birni a na ƙasar Mali da ke cikin wurare masu daɗɗaɗen tarihi na duniya, saboda haka ne ma a shekarar 1988, Cibiyar Al'adu, Ilimi da Kimiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta saka shi a sahun wurare mafi tasiri a duniya. Kaburan waliyai da ɗimbin littatafan tarihi a Timbuktu sun ɗaukaka sunan birnin da ke arewacin ƙasar Mali. Daga Timbuktu zuwa Bamako babban birnin ƙasar Mali akwai kimanin kilomita dubu ɗaya.Tairihi ya nuna cewar Abzinawa ne suka kafa wannan gari a cikin ƙarni na 11, yanzu muna ƙarni na 21, kenan Tombouctou…
Read More
Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

"Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi" Daga ISHAQ IDRIS GUIBI Gabatarwa Harshen Ingilishi yana ɗaya daga cikin manyan Harsunan duniya, da duniya ke taƙama da shi da tinƙaho. Harshe ne da Turawan mulkin mallaka suka ƙaƙaba wa ƙasashe renon Ingilishi. Ƙasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka irin su Nijeriya. Sai dai duk da cikarsa, da batsewarsa da haɗiye wasu harsuna, da gadar wasu harsuna, da satar kalmomin wasu harsuna, yana fama da yunwar wasu kalmomi, da rikicewar kalmomi da ma’anarsu. Har zan iya cewa Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi marasa shirbici da ruɗarwa.…
Read More
Alhasan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta Yamma a shekarar 1950

Alhasan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta Yamma a shekarar 1950

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhassan Ɗantata, fitaccen attajiri a faɗin nahiyar Afirika ta yamma, wanda tushen arzikinsa ya samo asali daga sayar da Goro da Gyaɗa. Haihuwa da nasaba; Alhassan Ɗantata ya fito ne daga cikin zuri’ar Agalawa, iyayensa fatake ne masu yawon kasuwanci daga wannan gari zuwa wancan. An haife shi a shekarar 1877, a wani ƙaramin ƙauye da ake kira Ɗanshayi a garin Bebeji, wanda ke da tazarar aƙalla kilomita goma sha-biyar daga garin Kano. Alhasan ɗaya ne daga cikin ’ya’yan Abdullahi wanda matarsa Fatima da ake kira Amarya ta haifa. Shi Abdullahi ɗa ne ga wani mutum…
Read More
Marubuta tamkar madubi muke ga al’umma – Zainab Sarauniyar Kanawa

Marubuta tamkar madubi muke ga al’umma – Zainab Sarauniyar Kanawa

"Wasu makaranta su ne ciwon kan marubuci" Daga ADAMU YUSUF INDABO Fitacciyar matashiyar marubuciya littafan adabin Hausa da ke cin kasuwar su a yanar gizo, wato Zainab Salihu Yarima da aka fi sani da 'Sarauniyar Kanawa' faɗi haka ne a yayin da take yin kira ga takwarorinta marubuta da su ji tsoron Allah su zama masu tsaftace alƙalumansu, don rubuta abun da zai zama mai amfanarwa ga al'umma bakiɗaya, wanda bai ci karo da addini da kuma al'adar Malam Bahaushe ba. Marubuciya Zainab Salihu Yarima (Sarauniyar Kanawa) dai ta yi wannan kira ne a yayin tattaunawarta da wakilinmu Adamu Yusuf…
Read More
Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A shekara ta 1839, an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma ɗan tireda daga Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amurka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo ƙarshen cinikin bayi a Amurka. Babu dai takamaimen lokacin da ake iya cewa shi ne lokaci da aka haifi Sengbe Pieh, sai dai masana tarihi sun yi ittifakin cewa, an haife shi ne a shekarar 1814 a ƙasar da a yanzu ake kira Saliyo. An yi imanin an haife shi a wani tsibiri da ke gundumar Bonthe, wajen da ya yi ƙaurin…
Read More