Adabi

Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

Harshen Ingilishi: Ga ƙoshi ga kwanan yunwa

"Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi" Daga ISHAQ IDRIS GUIBI Gabatarwa Harshen Ingilishi yana ɗaya daga cikin manyan Harsunan duniya, da duniya ke taƙama da shi da tinƙaho. Harshe ne da Turawan mulkin mallaka suka ƙaƙaba wa ƙasashe renon Ingilishi. Ƙasashen da Birtaniya ta yi wa mulkin mallaka irin su Nijeriya. Sai dai duk da cikarsa, da batsewarsa da haɗiye wasu harsuna, da gadar wasu harsuna, da satar kalmomin wasu harsuna, yana fama da yunwar wasu kalmomi, da rikicewar kalmomi da ma’anarsu. Har zan iya cewa Harshen Hausa ya fi Harshen Ingilishi wadatattun kalmomi marasa shirbici da ruɗarwa.…
Read More
Alhasan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta Yamma a shekarar 1950

Alhasan Ɗantata: Mutum mafi arziki a Afirika ta Yamma a shekarar 1950

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhassan Ɗantata, fitaccen attajiri a faɗin nahiyar Afirika ta yamma, wanda tushen arzikinsa ya samo asali daga sayar da Goro da Gyaɗa. Haihuwa da nasaba; Alhassan Ɗantata ya fito ne daga cikin zuri’ar Agalawa, iyayensa fatake ne masu yawon kasuwanci daga wannan gari zuwa wancan. An haife shi a shekarar 1877, a wani ƙaramin ƙauye da ake kira Ɗanshayi a garin Bebeji, wanda ke da tazarar aƙalla kilomita goma sha-biyar daga garin Kano. Alhasan ɗaya ne daga cikin ’ya’yan Abdullahi wanda matarsa Fatima da ake kira Amarya ta haifa. Shi Abdullahi ɗa ne ga wani mutum…
Read More
Marubuta tamkar madubi muke ga al’umma – Zainab Sarauniyar Kanawa

Marubuta tamkar madubi muke ga al’umma – Zainab Sarauniyar Kanawa

"Wasu makaranta su ne ciwon kan marubuci" Daga ADAMU YUSUF INDABO Fitacciyar matashiyar marubuciya littafan adabin Hausa da ke cin kasuwar su a yanar gizo, wato Zainab Salihu Yarima da aka fi sani da 'Sarauniyar Kanawa' faɗi haka ne a yayin da take yin kira ga takwarorinta marubuta da su ji tsoron Allah su zama masu tsaftace alƙalumansu, don rubuta abun da zai zama mai amfanarwa ga al'umma bakiɗaya, wanda bai ci karo da addini da kuma al'adar Malam Bahaushe ba. Marubuciya Zainab Salihu Yarima (Sarauniyar Kanawa) dai ta yi wannan kira ne a yayin tattaunawarta da wakilinmu Adamu Yusuf…
Read More
Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Sengbe Pieh: Bawan da ya yi wa Turawa tawaye

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A shekara ta 1839, an saci Sengbe Pieh, wani manomi kuma ɗan tireda daga Saliyo a matsayin bawa. Kan hanyar zuwa Amurka ya jagoranci tawaye a cikin jirgin ruwan jigilarsu, abin da ya kawo ƙarshen cinikin bayi a Amurka. Babu dai takamaimen lokacin da ake iya cewa shi ne lokaci da aka haifi Sengbe Pieh, sai dai masana tarihi sun yi ittifakin cewa, an haife shi ne a shekarar 1814 a ƙasar da a yanzu ake kira Saliyo. An yi imanin an haife shi a wani tsibiri da ke gundumar Bonthe, wajen da ya yi ƙaurin…
Read More
Kasuwancin littattafai a onlayin babban cigaba ne – Zulaihat Rano

Kasuwancin littattafai a onlayin babban cigaba ne – Zulaihat Rano

"Ta bincike da tunasarwar manyan marubuta nake samun hikimar rubutu" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Daga cikin marubutan Hausa da suka ci kasuwar littattafai tun zamanin adabin kasuwar Kano ke tashe, kuma yanzu suka dawo suka rungumi tsarin rubutun onlayin, akwai marubuciya Zulaihat Haruna Rano, daga Jihar Kaduna, wacce ta yi rubuce-rubuce da dama, masu ilimantarwa da nishaɗantarwa. A zantawarta da wakilin Blueprint Manhaja, Abba Abubakar Yakubu, ya tattauna da ita game da inda ta sa alqiblar rubutunta da kuma hasashenta kan cigaban harkar rubutun adabi, musamman yanzu da abubuwa suke komawa yanar gizo. Ga yadda hirar ta su ta kasance.…
Read More
Adamu Ɗan Maraya Jos

Adamu Ɗan Maraya Jos

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Ɗan Maraya Jos (an haife shi Adamu Wayya, 20 Disamba 1946 – 20 Yuni 2015) fitaccen mawaƙin Hausa ne daga Jos, Nijeriya. Ya shahara da salon waƙoƙinsa na musamman wanda ya haɗa waƙoƙin Hausa da jigogi da kayan kiɗa na zamani. An haifi Ɗan Maraya Jos a Sabon Gari, al’ummar Hausawa da suka fi yawa a garin Jos na Jihar Filato a Nijeriya. Ya girma a cikin gida na kiɗa kuma ya fara yin wasa tun yana ƙarami. Kakansa ne ya zaburar da shi, wanda ya kasance mawaƙin gargajiya na Hausa, ya kuma koyi yin kiɗa…
Read More
Sheikh Dakta Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya)

Sheikh Dakta Yusuf Ali (Sarkin Malaman Gaya)

An haife shi a cikin garin Gaya ta Jihar Kano a shekarar 1950. Ya haddace Alƙur'ani ya na da shekara 11, ya gama duk wani fanni na ilimi da ake karantawa a makarantun soro (ƙarshen ilimi kenan a wancan lokacin) yana da shekaru 15. Ya fara rubutun Alkur'ani yana da shekaru 13, ya zama Alaramma mai darasu tun ina da shekaru 14.Tsangayar sa tana nan a halin yanzu a Gashua, a Katuzu/Garin Yamma, jihar Yobe. Malam Musa Dan Dikkware shi ne Halifa sa mai darasu a halin yanzu. Ya fara shimfiɗa buzu na karantar da ɗalibai a makarantar soro tun…
Read More
Tarihin Marigayi Yusuf Maitama Sule, Ɗan Masanin Kano

Tarihin Marigayi Yusuf Maitama Sule, Ɗan Masanin Kano

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Sanin mutum sai Allah! Daga cikin mutane, akwai waɗanda Allah ke yi wa baiwar da bayyana ta ke da matuƙar wahala. Irin waɗannan mutane, rayuwarsu cike ta ke da darrusan da za a iya koya. Alhaji Yusuf Maitama Sule, Ɗanmasanin Kano, ɗaya ne daga cikin irin waɗannan mutane. Mutum ne mai ilimin addini da kuma na zamani. Allah ya yi masa baiwa da haƙuri, gaskiya, riƙon amana, cika alƙawari, sada zumunci, yafiya, barkwanci, dogaro da kai, da kuma sadaukar da kai. Mutum ne ɗan kishin ƙasa, mai son ganin jama’a sun ci gaba, mai son zaman…
Read More
Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa

Marigayi Sarkin Kano Muhammadu Rumfa

Daga SADIQ TUKUR GWARZO Cikakken sunan sa shi ne Muhammadu Rumfa ɗan Yaƙubi, sunan mahaifiyarsa Faɗimatu, ance ita mutuniyar ƙasar Rano ce. Muhammadu Rumfa nagartaccen mutum ne, adali, malami, wanda ba za a samu wani tamkarsa ba a cikin sha'anin mulkin Kano. Akwai zantuka game da yadda aka sanya masa suna RUMFA. Zance na farko na cewa saboda a saman Rumfa ake ajiye masa abinci sa'ar da ya zama sarki wai saboda dabbobi na zagayawa su lalata kafin ya baro fada. Na biyu kuma mafi inganci shine bisa kasancewarsa Rumfa majinginar 'yanuwansa da sauran al'umma, watau mai taimako da shiga…
Read More
Sharhin littafin ‘GAWA da RAI’

Sharhin littafin ‘GAWA da RAI’

Daga BAMAI A. DABUWA KKM Sunan Littafi: Gawa da Rai.Sunan Marubuci: Yusuf Yahaya Gumel.Shekarar Bugu: 2022.ISBN: Babu.Bugu: AGK Graphics Kurna.Yanayi: Ba A Fayyace ba.Jigo: Soyayya.Salo: Cikin Fage.Mai Sharhi: Bamai A. Dabuwa Kkm.Lambar Wayar Mai Sharhi: 07037852514.Email: [email protected] GABATARWA/TSOKACI. Littafin Gawa da Rai, labari ne na wani matashi (Anas), mai fama da larurar 'Cotard Delusion'. Wata kalar cuta ce, da idan ta kama mutum sai kawai ya gamsu a ransa cewa shi matacce ne ko kuma dai ya rasa wani sashe na jikinsa, alhalin ba hakan ba ne. Tauraron ya kamu da soyayyar wata yarinya (Laila). 'Yar gidan wani hamshaƙin mai…
Read More