Adabi

A yanzu ana kallon marubuci kamar wanda bai san kansa ba – Ayusher Muhammad

A yanzu ana kallon marubuci kamar wanda bai san kansa ba – Ayusher Muhammad

"Kaso sittin bisa ɗari Ina wa rubutu kallon sha’awa ne" DAGA MUKHTAR YAKUBU Aisha Muhammad Salis, wadda aka fi sani da Ayusher Muhammad a harkar rubutun onlayin, ta na daga cikin fitattun marubutan soshiyal midiya da a yanzu ake yayin su. Haka kuma tana da basira da salon kirkirar labari da rubutawa. Don haka ne ma ta yi fice a cikin marubutan da ake ji da su a onlayin. Domin jin ko wacece Ayusher, wakilin Blueprint Manhaja a Kano, ya tattauna da ita, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance. MANHAJA: Da farko dai za…
Read More
Jagora ya yaba wa Hamisu Ibrahim kan rubuta littafin koyar da Larabci da Turanci

Jagora ya yaba wa Hamisu Ibrahim kan rubuta littafin koyar da Larabci da Turanci

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Kwamared Adam Abubakar Adam wanda aka fi sani da Jagora, daya daga cikin jagororin Kungiyoyin Ci Gaban Al'umma a Karamar Hukumar Nasarawa Jihar Kano ya yaba wa hazikin marubucin nan Malam Hamisu Ibrahim wanda ya bada gudunmawa wajen rubuta littafi wanda ya kunshi kalmomin Larabci zuwa Turanci domin amfanin masu son koyon Larabci tun daga tushe kamar dai yadda Jagoran ya bayyana cewa wannan ba karamin aiki ba ne da zai taimaka wa wadanda suka san Turanci su koyi Larabci a matakin farko. Jagora ya kara da cewa "akwai bukatar marubutanmu su yi amfani da…
Read More
Tarihin Alhaji Musa Ɗan Ƙwairo

Tarihin Alhaji Musa Ɗan Ƙwairo

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Alhaji Musa Dan Kwairo ya kasance fitaccen mawakin kasar Hausa kuma mai matukar daraja. An haife shi ne a garin Bakura na Jihar Zamfara a Nijeriya a farkon shekarar 1909. Hazakar Musa Dan Kwairo ta fannin waqa da sha’awar wakokin gargajiya ta fito ne tun yana karami, kuma zai cigaba da zama daya daga cikin fitattun jarumai a wannan fanni. Wakar gargajiyar Hausa tana da matukar muhimmancin al’adu a yankin arewacin Nijeriya, kuma Musa Dan Kwairo ya taka muhimmiyar rawa wajen kiyayewa da kuma habaka wannan al’adun gargajiya. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen samar da kyawawan…
Read More
Nazari: Yadda Gasar Hikayata ta BBC Hausa ke ɗaukaka muryar mata 

Nazari: Yadda Gasar Hikayata ta BBC Hausa ke ɗaukaka muryar mata 

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU "Ta dalilin wannan gasa ta Hikayata da BBC Hausa suke shiryawa mata marubuta da a baya ba a san da su ba, yanzu sunan su ya fito. Tabbas gasar tana ɗaga muryar mata ta yadda za su isar da kukansu da bayar da shawarwari na hanyoyin inganta rayuwar mata da zamantakewar al'umma." Aisha Adam Hussaini kenan ƴar shekara 27 da ta fito daga Jihar Kano, wacce ta zama gwarzuwa ta ɗaya a Gasar Hikayata ta BBC Hausa ta 2023, yayin da take yabawa da yadda ake gudanar da gasar rubuta gajeren labari ta marubuta mata.  "Na…
Read More
Marubutan Arewa sun yi taron alhinin rasuwar Sheikh Yusuf Ali

Marubutan Arewa sun yi taron alhinin rasuwar Sheikh Yusuf Ali

DAGA MUKHTAR YAKUBU An bayyana fitaccen malamin addinin Musluncin nan marigayi Sheikh Dakta Yusuf Ali wanda Allah ya yi wa rasuwa a farkon watan Nuwamban da ya gabata a matsayin wani managarcin malamin da ya yi shaharar da za a daɗe ba a manta da shi ba a fannin ilimi da kuma mu'amala da jama'a Wannan bayanin ya fito ne daga bakin shugaban majalisar malamai ta Arewa da kuma ta Jihar Kano Sheikh Ibrahim Khalil a lokacin da yake gabatar da jawabin sa a wani taro da gamayyar ƙungiyar marubutan Arewa da ƙungiyar ANA ta ƙasa reshen Jihar Kano suka shirya…
Read More
Asalin Kaduna daga tushe

Asalin Kaduna daga tushe

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Zagayen wani kogi da ake kira Kadduna, akwai wasu ƙauyuka da mutane ke zaune warwatse a gurin. Daga cikin irin waɗannan jama'a akwai ƙabilu da suka fi yawa kamar irin su Gbagyi wanda Bahaushe yake kira Gwari, da kuma Fulani. Gwarawa na zaune a ƙauyen Kudanda, wanda yanzu ya zama Kakuri, Fulani kuma ta nasu ɓangaren suna zaune a Kukogi wanda yanzu ta koma Gworo. Wannan kogi matattara ce ta kadoji wanda hakan ta jawo ake kiran sa da suna Kadduna, ita kuma wannan kalma ta Kadduna, jama'un kalmar kada ce, wacce ma'anarta ita ce kadodi…
Read More
Marubuta na taka muhimiyyar rawa a zamantakewar aure – Binta Umar Abbale

Marubuta na taka muhimiyyar rawa a zamantakewar aure – Binta Umar Abbale

"Marubuta na fuskantar ƙalubalen satar fasaha" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Marubuta mutane ne masu martaba da kwarjini, waɗanda Allah Ya yi wa bai wa ta abubuwa daban-daban da suke amfanar da jama'a. Binta Umar Abbale na daga cikin irin marubutan da jama'a da dama ke ƙaruwa da ita. Bayan kasancewarta marubuciya, ƴar kasuwa, tana kuma bada shawarwari ga mata ta yadda za su gyara kansu da zamantakewar aurensu. Binta Abbale wacce ita ce shugabar ƙungiyar marubuta ta Manazarta Writers Association ta rubuta littattafai 19 da suka ƙunshi labarai masu ɗauke da darussa na faɗakarwa da nishaɗantarwa. A ganawarta da wakilin…
Read More
Ko kun san daga ina ilimin lissafi ya samo asali?

Ko kun san daga ina ilimin lissafi ya samo asali?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Duk da cewa babu wanda ya san asalin inda ilimin lissafi ya samo asali, amma a yau Blueprint Manhaja za ta yi duba ne kai tsaye zuwa ga ilimin lissafi, duk da cewa babu wani abu da ya rage game da daɗaɗɗen wajen tarihin lissafi da aka lalata a ƙarni na 13, amma mun binciko tare tattaro bayanan masana dangane da inda wajen yake da kuma yadda wajen yake. Sanin asalin ilimin lissafi abu ne mai wahalar gaske amma an fara ganin lissafai masu wahala ne a kusan shekara ta 3000 kafin bayyanar Annabi Isa (300…
Read More
Bambancin marubutan onlayin da mawallafa littattafai a bayyane yake – Milhart

Bambancin marubutan onlayin da mawallafa littattafai a bayyane yake – Milhart

"Ban yi wa marubuta adalci ba, idan na ce suna da girman kai" Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU Fadeela Yakubu matashiyar marubuciyar onlayin ce daga Jihar Gombe, wacce za a iya kiranta da ƴar baiwa, saboda yadda take da basira da hikimar yin abubuwa da dama a fagen ƙirƙira, domin ilimantar da matasa, faɗakarwa da kuma nishaɗantarwa. Bayan kasancewarta marubuciya, Fadeela, wacce ake kira da Milhart, sananniya ce a manhajar Tiktok da YouTube, inda take wallafa kalaman soyayya da faɗakarwa, da kuma karanta littattafan Hausa. Allah Ya yi mata baiwa ta zaƙin murya ta yadda take amfani wannan baiwar da Allah…
Read More
Wane ne Adolf Hitler?

Wane ne Adolf Hitler?

Daga MAHDI M. MUHAMMAD An haifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afirilu na shekara 1889, ya kashe kansa ranar 30 ga watan Afirilu na shekara 1945 bayan an ci Jamus da yaƙi. An aifi Adolf Hitler ranar 20 ga watan Afrilu na shekara 1889 wato shekaru 122 kenan da suka gabata. An aife shi a wani gari mai suna Braunau-am Inn, a ƙasar Austriya kusa da iyakar ƙasar da Jamus. Shi ne na huɗu a gidansu. Mahaifinsa wani jami'in Custum ne, ya rasu a yayin da Hitler ke da shekaru 14 da aihuwa. Marubuta tarihin Hilter sun ce bai…
Read More