09
Apr
Daga MUKHTAR YAKUBU Gamayyar marubuta a ƙarƙashin ƙungiyar marubuta ta Kano Literary Space sun shirya Gagarumin Bikin Taya Murna ga Sarkin Adabin Harshen Hausa Dr. Aminu Alan Waƙa wanda a kwanakin baya Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk ya naɗa shi sarautar Sarkin Adabin ƙasar Hausa. Taron mai taken ‘Adabi Mabuɗin Al'adu’, an gudanar da shine a ranar Asabar, 28 ga Maris, 2026, a da ɗakin taro na CITAD dake birnin Kano, inda manyan masana harshen Hausa da adabi suka gabatar da jawabai da waƙoƙi akan abubuwan da suka shafi tarihi da kuma al'adunmu na gargajiyar Hausa. Tun da farko da…
