Siyasa

Ba mu yarda da ci gaban shugabanci mara kan gado ba – PDP

Ba mu yarda da ci gaban shugabanci mara kan gado ba – PDP

Daga AISHA ASAS Babbar jam'iyyar bamayya a Nijeriya, PDP, ta ce duk da dai tana yi wa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari barka da dawowa daga jinyar da ya je a Turai, amma ba ta yi na'am da zancen shugaban ba na cewa 'yan Nijeriya su sa ran ganin "Ci gaba." A bayanin da ta fitar, PDP ta ce tana ra'ayin ko ma dai da wata manufa shugaban ya furta kalmar 'Ci gaba' ɗin, kada hakan ya yi nasaba da barin mulkinsa ya zuwa 29, Mayu, 2023. Ta ci gaba da cewa hasali ma 'yan Nijeriya ba su yarda da duk…
Read More
Cross River: Shirin sauya sheƙar Gwamna Ayade ya kaɗa hanjin PDP

Cross River: Shirin sauya sheƙar Gwamna Ayade ya kaɗa hanjin PDP

Daga UMAR M. GOMBE Domin gudun kada ta rasa ɗanta, Jam'iyyar PDP ta tura a rarrashi Gwamnan Jihar Cross River, Ben Ayade,bayan da ta gano cewa gwamnan na shirin sauya sheƙa zuwa APC. Binciken Manhaja ya gano cewa matakin sauya sheƙar da Gwamna Ayade ya ɗauka ba ya rasa nasaba da rasa ƙarfin ikon jan akalar PDP a jihar ga 'yan majalisar ƙasa daga jihar kamar yadda ya bayyana yayin wani taro da suka gudanar kwannan nan. Haka nan, Manhaja ta tattaro cewa ɗaukacin shugabannin ƙananan hukumomin jihar su 18 da kansilo196 ba su saɓa wa umarnin gwamnan saboda cikakkiyar…
Read More
Kebbi: Wasu jigogin APC sun buƙaci a yi karɓa-karɓa game da kujerar gwamna

Kebbi: Wasu jigogin APC sun buƙaci a yi karɓa-karɓa game da kujerar gwamna

Daga FATUHU MUSTAPHA Wasu masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a jihar Kebbi, sun yi motsi tare da ɗauko batun karɓa-karɓa game da sha'anin shugabancin jihar a tsakanin shiyoyin jihar. Da yake yi wa manema labarai bayani jim kaɗan bayan kammala ganawa da masu faɗa a ji na APC daga shiyoyin sanata na Kudu da Arewa na jihar, mai magana da yawun haɗakar kuma Kwamishinan Hukumar Kula da Ma'aikatan Gwamnatin Jihar, Alhaji Abdullahi Mohammed, ya ce manufarsu ita ce yadda za a tafi da kowa amma babban burinsu shi ne yadda za a riƙa kewayawa da keuerar gwamna ana…
Read More

Tinubu da ƙurar 2023 a Arewa

Tinubu Daga FATUHU MUSTAPHA ’Yan makonni da suka wuce ne, Gidan Arewa, wato Arewa House, da yake a Kaduna ya bayar da sanarwar tsohon gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, zai zama babban baƙo mai jawabi a taron da take shiryawa na shekara-shekara, don tunawa da Sir Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato, na wannan shekara. Tun bayan da wannan sanarwa ta fito, aka fara cece-kuce a Arewacin ƙasar akan wannan zaɓi na tsohon sanatan. Jim kaɗan bayan taron kuma sai ga wata sanarwar daga hukumomi na cewa, za a yi bikin taya jagoran na APC murnar zagoyawar ranar…
Read More
Matawalle: APC ta yi babban kamu a Zamfara

Matawalle: APC ta yi babban kamu a Zamfara

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya kammala shirin sauya sheƙa daga jam'iyyarsu ta PDP zuwa APC inda ake sa ran shugaban riƙo na APC, Mai Mala Buni ya gabatar da shi ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari. Bayanan da Manhaja ta kalato sun nuna mai yiwuwa a kammala komai idan tawagar Gwamnatin Tarayya ta ziyarci Zamfara a ranar Talata domin jajanta wa gwamnan game da ibtila'in gobarar kasuwa da ya auku kwannan nan a jihar. Tun ba yau ba, wasu gwamnoni masu ci tare da tsohon gwamnan Zamfara, Ahmed Sani Yerima, na daga cikin gaggan 'yan siyasar da…
Read More
Za a fara rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni

Za a fara rajistar masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za a ci gaba da aikin rajistar katin masu zaɓe a ranar 28 ga Yuni, 2021. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka ga manema labarai a taron da ya yi da su a hedikwatar hukumar a Abuja a ranar Alhamis. Mahmood ya ce, “Bayan mun duba waɗannan matsaloli da matakan da mu ka ɗauka don magance su, yanzu hukumar ta kai matsayin da za ta iya bayyana Litinin, 28 ga Yuni, 2021 a matsayin ranar da za mu koma mu ci gaba…
Read More
Neja: PDP ta dakatar da Babangida Aliyu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

Neja: PDP ta dakatar da Babangida Aliyu bisa zargin yi wa jam’iyya zagon-ƙasa

Daga AISHA ASAS Jam'iyar PDP a Jihar Neja ta bayyana dakatar da Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Dakta Mu'azu Babangida Aliyu. PDP ta Ƙaramar Hukumar Chanchaga ta dagatar da Aliyu ne bisa wasu zarge-zarge a kansa ciki har da haifar da rashin jituwa a tsakanin shugabannin jam'iyyar. Kazalika, an zargi Tsohon Gwamnan da yi wa jam'iyya zagon-ƙasa, sai batun rashin martaba faɗar Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai, wanda ya buƙaci a haɗu a gudanar da babban taron jam'iyya na jiha. Haka nan, akwai zargin cewa Dr Mu'azu Babangida Aliyu ya tallafa wa APC da kuɗi Naira milyan N450 yayin zaɓen…
Read More
Ihejirika ya zama ɗan APC

Ihejirika ya zama ɗan APC

Daga WAKILINMU Shugaban Kwamitin Riƙo na APC kuma Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya karɓi tsohon Shugaban Rundunar Sojoji Lt.Gen. Oyeabo Azubike Ihejirika (mai murabus) a jam'iyyarsu ta APC. Manhaja ta gano cewa, tun bayo na Ihejirika ya soma raɓar APC inda sai a wannan lokaci ya tsunduma cikinta a bayyane. Sanarwa da ta fito ta hannu Daraktan Yaɗa Labarai ga Buni, Mamman Mohammed, ta nuna an gabatar da Gen. Ihejirika a hukumance ga shugaban riƙo na jam'iyyar APC a Juma'ar da ta gabata a bisa jagorancin Gwamnan Jigawa, Alhaji Abubakar Badaru da Hon. Farouk Adamu Aliyu. Buniya ce,…
Read More
Kotu ta ɗaure Farfesa kan maguɗin zaɓe a Akwa-Ibom

Kotu ta ɗaure Farfesa kan maguɗin zaɓe a Akwa-Ibom

Daga UMAR M. GOMBE Wata babbar kotu a jihar Akwa-Ibom ta yanke wa Farfesa Peter Ogban hukuncin zaman kaso na shekara uku bayan da ta kama shi da laifin tafka maguɗin zaɓe. Kotu ta kama malamin da laifin shirya sakamakon zaɓe na ƙarya tare da sanar da sakamakon yayin babban zaɓen 2019 a matsayinsa na shugaban zaɓe a shiyyar Akwa-Ibom ta Arewa maso-yamma. Farfesan wanda malami ne a Jami'ar Calabar a Sashen Nazarin Harkokin Noma, ya tafka maguɗi wajen haɗa sakamon wasu ƙananan hukumomi guda biyu a wancan lokaci, wato ƙaramar hukumar Oruk Anam da Etim Ekpo. A can baya,…
Read More
Alaƙar Buhari da Tinubu tana ƙara armashi – Fadar Shugaban Kasa

Alaƙar Buhari da Tinubu tana ƙara armashi – Fadar Shugaban Kasa

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya musunta zargin da ake yaɗawa kan cewa ruwa ya yi tsami tsakaninsa da tsohon Gwamnan Jihar Legas kuma jigo a jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu. Buhari ya musunta zargin hakan ne ta wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya fitar inda ya bayyana cewa hakan ba gaskiya ba ne. Sanarwar ta nuna cewa, hasali ma alaƙar da ke tsakanin dattawan biyi sai armashi da ƙarƙo take ƙarawa. A cewar Shehu Garba, “Fadar Shugaban Ƙasa na faɗa da babbar murya cewa babu wani rashin jituwa a tsakanin Shugaba Muhammadu Buhari…
Read More