20
Apr
Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi barazanar za ta hukunta duk wata jam'iyyar siyasa wadda ta kasa gudanar da babban taron ta (congress) cikin lumana. A cikin wata sanarwa da ta bayar a ranar Litinin, INEC ta ce akwai yiwuwar ba za ta amince da sakamakon da aka samar a babban taron jam'iyyar da aka yi a cikin hatsaniya ba idan har ba a daina wannan ɗabi'ar ba. Kakakin hukumar, Mista Festus Okoye, ya ce ƙazancewar rikicin da ake samu a wajen babban taron jam'iyya ya na sanyawa hukumar ta samu “matuƙar wahala” wajen gudanar da aikin…
