18
May
Daga FATUHU MUSTAPHA Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo, ya ce shi dai bai bayyana ra'ayinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa ba a 2023. Yana mai cewa ɗaga wanna zance a yanzu neman karkatar da hankali ne kawai. Sanarwa da mai magana da yawun Osinbajo, Laolu Akande ya fitar a Litinin da ta gabata, ta nuna ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ba shi da alaƙa da wani gangamin goyon bayan tsayawa takara da aka shirya ta intanet. Sanarwar ta ce, "Hankalin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa ya kai ga wani shafin intanet 'supportosinbajo.ng' wanda ke kira ga 'yan Nijeriya da su zo a haɗa…
