09
Jun
Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala A.Mohammed CON (Ƙauran Bauchi), ya rushe majalisarsa tare da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar. Sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Mukhtar Gidado, ta nuna Bala ya sauke duka kwamishinoninsa haɗa da wasu masu riƙe da muƙaman siyasa da suka haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jihar da dukkanin Masu Bai wa Gwamna Shawara (SA) amma ban da wasu mutum huɗu daga ckinsu. Mutum huɗu da suka tsira da muƙamansu su…
