Siyasa

APC ta lashe zaɓen maye gurbi a Jigawa

APC ta lashe zaɓen maye gurbi a Jigawa

Daga UMAR AƘILU MAJERI a Dutse Jam'iyyar PDP da sauran jam'iyyu sun sha ƙasa a zaɓen maye gurbi na ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Gwaram da aka gudanar a jihar Jigawa ran Asabar da ta gabata. Ɗan takarar jam'iyyar APC, Yusif Shitu Galanbi, ya samu nasarar lashe zaɓen ne inda ya yi nasarar a kan abokan hamayyarsa na PDP, Sharif Kamilu Maicalbi da sauransu. Wannan shi ne karo na uku da Galanbi zai wakilci al'ummar yankinsu a Majalisar Wakilai ta Ƙasa. Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Galanbi a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen. Jami'in Hukumar…
Read More
Jam’iyyu 18 ke fafutikar neman kujerar gwamnan Anambra – INEC

Jam’iyyu 18 ke fafutikar neman kujerar gwamnan Anambra – INEC

Daga UMAR M. GOMBE Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce jam'iyyun siyasa 18 ne su ka nuna sha'awar su ta shiga zaɓen gwamnan Jihar Anambara da za a yi a ranar 6 ga Nuwamba mai zuwa. Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wajen taron kwata ta biyu na hukumar da jam'iyyun siyasa wanda aka yi a ranar Alhamis a Abuja. Yakubu ya ce dukkan jam'iyyun 18 sun tsara gudanar da zaɓuɓɓukan su na fidda gwani a bisa jadawalin kwanaki da hukumar ta fitar. Ya ce, “A kan batun zaɓuɓɓukan ƙananan hukumomin Yankin Birnin Tarayya, jam'iyyun siyasa…
Read More
INEC ta sa ranakun zaɓen gwamnonin Ekiti da Osun

INEC ta sa ranakun zaɓen gwamnonin Ekiti da Osun

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa za ta gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Ekiti a ranar 18 ga Yuni, 2022 yayin da kuma za ta yi na gwamnan Jihar Osun a ranar 16 ga Yuli, 2022. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a wurin taron da ya yi da kwamishinonin zaɓe na jihohi a ranar Laraba a hedikwatar INEC da ke Abuja. Yakubu ya ce an wallafa ranakun da aka aje na fara yaƙin neman zaɓe da sauran cikakkun bayanai kan jadawalin ranakun zaɓen da sauran ayyuka dangane da zaɓuɓɓukan biyu a gidan…
Read More
APC ta dakatar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Birnin Kano

APC ta dakatar ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Birnin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Jam'iyyar APC ta jihar Kano ta ce ta dakatar da ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Sha'aban Ibrahim Sharaɗa daga jam'iyya na tsawon shekara guda. Jam'iyyar ta ce daga wannan lokaci, ta haramta wa ɗan Majalisar shiga harkokinta a dukkanin matakai na tsawon lokacin dakatarwar. Cikin sanarwar da ta sami sa hannun Shugaban APC na gundumar Sharaɗa, Aljahi Abdullahi Umar da sakatarensa Auwalu Saidu Muhammad, mai ɗauke da kwanan wata 16/06/2021, APC ta ce ta ɗauki matakin dakatar da Hon Sha'aban ne bayan da aka same shi da aikata laifin cin mutuncin Mai Girma Gwamnan Kano da…
Read More
Bayan shekara 25, Nijeriya ta samu ƙarin rumfunan zaɓe 56,872

Bayan shekara 25, Nijeriya ta samu ƙarin rumfunan zaɓe 56,872

Daga AMINA YUSUF ALI Hukumar Zaɓe ta Kasa (INEC) ta ce kawo yanzu adadin rumfunan zaɓe da Nijeriya ke da su ya kai 176,846. Tun 1996 da aka ƙirƙiri ƙarin rumfunan zaɓe, hakan bai sake aukuwa ba sai bayan shekara 25, inda INEC ta sauya wasu cibiyoyin zaɓe guda 56,872 a faɗin ƙasa zuwa cikakkun rumfunan zaɓe. Kafin wannan lokaci, rumfunan zaɓen da INEC ta san da su a faɗin ƙasa guda 119,974 ne. Da yake jawabi a wajen wani taro tare da kwamishinonin hukumar a ranar Laraba, Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce sun yi nasarar ɗauke rumfunan…
Read More
Yulin 2022 zaɓen gwamna zai gudana a Osun – INEC

Yulin 2022 zaɓen gwamna zai gudana a Osun – INEC

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta ce, ya zuwa 16 ga Yulin 2022 za a gudanar da zaɓen gwamnan na jihar Osun. Bayanin haka na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da INEC ta fitar ta hannun sakatariyarta, Rose Oriarian-Anthony a Talatar da ta gabata. Jadawalin zaɓen mai ɗauke da kwanan wata Yuni 10, 2021, ya nuna tsare-tsaren ayyukan zaɓen wanda za a soma gudanarwa daga 1 ga Fabrairun 2022.
Read More
Gona zan koma bayan na yi murabus daga siyasa – Masari

Gona zan koma bayan na yi murabus daga siyasa – Masari

Daga BASHIR ISAH Gwamna Aminu Masari na jihar Katsina, ya ce zai yi murabus daga harkokin siyasa bayan kammala wa'adinsa  a matsayin gwamna. Masari ya bayyana haka ne sa'ilin da yake yi wa taron maneman labarai bayani a Katsina yayin bikin Ranar Dimukuraɗiyya na bana da ya gudana ran Asabar da ta gabata. Gwamnan ya ce bayan kammala mulkinsa zai yi murabus daga siyasa sannan ya koma gonarsa ya ci gaba da noma. A cewarsa, "Na riƙe muƙamai da dama kama daga matsayin kwamishina a jihar Katsina zuwa Majalisar Ƙasa inda na riƙe matsayin Shugaban Majalisar Wakilai. “Ga shi har yanzu…
Read More
Ranar Dimukuraɗiyya: Mun cire ‘yan Nijeriya milyan 10 daga ƙangin talauci cikin shekara biyu – Buhari

Ranar Dimukuraɗiyya: Mun cire ‘yan Nijeriya milyan 10 daga ƙangin talauci cikin shekara biyu – Buhari

Daga AISHA ASAS Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, ya ce gwamnatinsa ta yi nasarar cire 'yan Nijeriya su milyan 10.5 daga ƙangin talauci a tsakanin shekaru biyu da suka gabata. Buhari ya bayyana haka ne a jawabinsa na Ranar Dimukuraɗiyya ta bana da ya gabatar wa 'yan Nijeriya a ranar Asabar. Bayanan Bankin Duniya sunan Nijeriya na daga cikin ƙasashen da suke da mutane masu fama da matsanancin talauci. Idan dai za a iya tunawa, a 2019 Buhari ya yi alƙawarin raba 'yan Nijeriya milyan 100 da talauci a cikin shekaru goma. Yayin jawabinsa na ran Asabar shugaban ya ce, "Duk…
Read More
Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen kwamishinonin INEC da zai naɗa

Buhari ya aika wa Majalisar Dattawa sunayen kwamishinonin INEC da zai naɗa

Shugaba Muhammadu Buhari ya tura sunayen mutane shida da ya ke so ya naɗa a matsayin kwamishinonin Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ga Majalisar Dattawa domin ta amince da zaɓen su da ya yi. Sun haɗa da Lauretta Onochie, wadda ita ce mai ba shi shawara ta musamman kan soshiyal midiya. A da dai majalisar ta yi fatali da zaɓin da ya yi wa Onochie a zaman ta na ranar 12 ga Oktoba, 2020 domin wasu sanatoci sun ce ba su amince da naɗin nata ba. A zaman majalisar na ranar Laraba ta wannan makon, Sanata Yahaya Abdullahi (ɗan APC daga mazaɓar…
Read More
Gwamna Bala ya sauke kwamishinoninsa da masu riƙe da muƙaman siyasa

Gwamna Bala ya sauke kwamishinoninsa da masu riƙe da muƙaman siyasa

Daga AISHA ASAS Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala A.Mohammed CON (Ƙauran Bauchi), ya rushe majalisarsa tare da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa a jihar. Sanarwar manema labarai da ta fito ta hannun mai bai wa gwamnan shawara kan sha'anin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a, Mukhtar Gidado, ta nuna Bala ya sauke duka kwamishinoninsa haɗa da wasu masu riƙe da muƙaman siyasa da suka haɗa da Sakataren Gwamnatin Jihar da Shugaban Ma'aikatan Fadar Gwamnatin Jihar da dukkanin Masu Bai wa Gwamna Shawara (SA) amma ban da wasu mutum huɗu daga ckinsu. Mutum huɗu da suka tsira da muƙamansu su…
Read More