05
Jul
Daga SANUSI MUHAMMAD, a Gusau A ranar Talata, 29 ga Yunin da ya gabata gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC. Gwamnan ya ba da sanarwar komawsrsa APC neyayin wani ƙasaitaccen gangami da aka shirya don karɓar sa a APC ƙarƙashin jagorancin shugan jam'iyyar na ƙasa, Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe. Matawalle, ya zama gwamnan Zamfara ne a 2019 biyo bayan wani hukunci da Kotun Ƙoli ta yanke kan rikicin cikin gidan da APC ta yi fama da shi a lokacin zaɓen fidda gwani a 2019. Yayin gangamin an ji Matawalle na…
