19
Jul
Wata Babbar Kotun Tarayya a Abuja ta dakatar da Majalisar Dokokin Jihar Zamfara daga shirinta na neman tsige Mataimakin Gwamnan Jihar, Mahdi Gusau. Alƙali Obiora Egwuatu shi ne ya ba da wannan umarni a yau Litinin yayin da yake yanke hukunci kan ƙarar da jam'iyyar PDP ta shigar ta hannun lauyanta, Ogwu Onoja, SAN. Cikakken bayani na nan tafe.
