28
Aug
Jam'iyyar PDP ta ba da sanarwar cewar za ta gudanar da babban taronta na ƙasa tsakanin ranar 30-31 ga Oktoba mai zuwa idan Allah Ya kai mu. Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, Aminu Tambuwal ne ya shaida wa manema labarai hakan jim kaɗan bayan kammala wani taronsu a Abuja a jiya Juma'a. Tambuwal ya ce za su miƙa shawarwarinsu dangane da taron ga shugabancin jam'iyyar na ƙasa, tare da cewa shugabannin ne za su tsayar da inda taron zai gudana. Kazalika, Tambuwal ya ce sun haɗa wata tawaga ta mutum takwas ƙarƙashin jagorancin tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Marka, da…
