09
Oct
Daga BASHIR ISAH An rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar Nasarawa su 13 bayan kammala zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a Larabar da ta gabata. Gwamnan jihar, Injiya Abdullahi A. Sule ne ya rantsar da ciyamomin a fadar gwamnatin jihar da ke Lafia, babban birnin jihar a jiya Juma'a. Yayin rantsarwar, Gwamna Sule ya nusar da sabbin ciyamomin da su sani wannan wata muhimmiyar dama ce suka samu don bada gudunmawarsu ga cigaban jihar da ma al'ummarta. Don haka ya hore su da su yi aiki bilhaƙƙi tare da kwatanta adalci wajen sauke nauyin al'umma da ya…
