Siyasa

Taron PDP: Muna da damar daidaita Nijeriya – Atiku

Taron PDP: Muna da damar daidaita Nijeriya – Atiku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a Abuja ya buƙaci ɗaukacin 'yan Nijeriya da su yi amfani da damar da jam’iyyar PDP ta bayar wajen daidaita Nijeriya da ceto ƙasar daga halin da ta ke ciki. Atiku ya ba da wannan cajin ne ga wakilai da jami'an jam'iyyar a babban taron jam'iyyar PDP na 2021. A cewarsa, akwai bambance-bambance da dama, amma 'yan Nijeriya za su iya cimma komai idan suka ajiye saɓanin da ke tsakaninsu a gefe. Ya ƙara da cewa, taron wata dama ce ta yanke…
Read More
Me ya sa Jonathan ya zille wa babban taron PDP?

Me ya sa Jonathan ya zille wa babban taron PDP?

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Shugaban Ƙasar Nijeriya, Mista Goodluck Ebele Jonathan, wanda ɗa ne ga jam'iyyar adawa ta PDP, ana zargin shi da zille wa babban taron da jam'iyyar ta gudanar a jiya Asabar a Babban Birnin Tarayya, Abuja. Ranar Juma'a kwana ɗaya kafin babban taron na jam'iyyar PDP, Jonathan ya bayyana cewa zai bar Abuja zuwa Nairobi, Ƙasar Kenya domin halartar taron Ƙungiyar Haɗin Kan Afrika akan bunƙasa zaman lafiya, tsaro da kuma cigaban yankin. Sai dai kuma, wasu daga cikin 'ya'yan jam'iyyar PDP sun yi amannar cewa Jonathan ya ƙirƙiri tafiyar ne kawai a daidai…
Read More
Ku zo mu haɗa hannu mu ceci Nijeriya, cewar PDP ga ‘yan Nijeriya

Ku zo mu haɗa hannu mu ceci Nijeriya, cewar PDP ga ‘yan Nijeriya

Daga BASHIR ISAH Gwamnan Jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya babban taron jam'iyyar PDP, Ahmadu Fintiri, ya yi kira ga 'yan Nijeriya da su zo su haɗa hannu da jam'iyyarsu don karɓe mulkin ƙasa da kuma gyara wa ƙasar zama. Fintiri ya yi wannan kira ne a lokacin da yake jawabin maraba da dalaget da jami'an jam'iyya wajen babban taron PDP na 2021 ranar Asabar a Abuja. Yana mai cewa, babban taron nasu shi ne mataki na farko na shirin ceto Nijeriya da jam'iyyarsu ta yi. Ya ce, “Za mu karɓe ƙasarmu kamar yadda muka saba. Ya kamata mu ceto…
Read More
PDP Za Ta Amshi Mulki A 2023, Inji Saraki

PDP Za Ta Amshi Mulki A 2023, Inji Saraki

Daga NASIR S. GWANGWAZO Tsohon shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya, ka tsohon gwamnan Kwara, Dr. Abubakar Bukola Saraki a shirye PDP ta ke ta ƙwace mulki a shekarar 2023. Saraki ya faɗi haka ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi yau Talata da gidan talabijin na AriseTv. Tsohon Shugaban Majalisar ta Dattawa ya bayyana cewa a yanayin yadda Nijeriya take a rarrabe, zai ba PDP dama ta lashe zaɓen 2023. Ya ce, Nijeriya ba ta faɗa wa hali da yanayin rarraba ba irin na wannan lokaci a ƙarƙashin mulkin Buhari. "Muna da duk wani abu da ake buƙata don…
Read More
Rashin amfana da mulkin Buhari ya sa ‘yan Arewa ƙin jinin tsarin karɓa-karɓa – Na’Abba

Rashin amfana da mulkin Buhari ya sa ‘yan Arewa ƙin jinin tsarin karɓa-karɓa – Na’Abba

Daga BASHIR ISAH Tsohon shugaban Majalisar Wakilai ta Ƙasa, Ghali Umar Na’Abba, ya bayyana cewa galibin 'yan Arewa na kallon mulkin Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a matsayin salwantar da muhimmiyar damar da ta samu ga yankinsu. Na'Abba ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a cikin shirin siyasa a tashar talabijin ɗin Daily Trust, inda ya ce da daman 'yan Arewa na ƙin tsarin mulki na karɓa-karɓa ne ba don komai ba sai don ganin cewa babu wani amfani da suka samu a mulkin Buhari. Tsohon shugaban majalisar ya ce, Buhari mutum ne mai…
Read More
Buhari ya yaba da zaɓukan APC a Katsina

Buhari ya yaba da zaɓukan APC a Katsina

Daga UMAR GARBA a Abuja Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓukan shugabannin jam'iyar APC a Katsina tun daga matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi har zuwa matakin jiha. Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka a lokacin da kwamitin shirya zaɓukan shugabannin jam'iyyar ya miƙa rahotonsa na ƙarshe bayan kammala aikinsa. Kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin shugaban ma'aikatan fadar gidan gwamnati na Katsina, Muntari Lawal da haɗin gwiwa da kwamitin shirya zaɓukan daga uwar jam'iya ta ƙasa. Masari ya kuma bayyana cewar Shugaba Buhari ya yi matuƙar farin ciki bisa ga yadda aka…
Read More
Babakeren Ganduje ya yi yawa, inji Malam Shekarau

Babakeren Ganduje ya yi yawa, inji Malam Shekarau

Daga BASHIR ISAH  Tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma sanata mai wakiltar Kano ta Tsakiya, Malam Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano), ya ce, sun shigar da kukansu ga uwar jam’iyyarsu ta APC a mataki na ƙasa ne kan yadda a ke gudanar da harkokin jam’iyyar tasu ba tare da sako su ciki ba daga ɓangaren jihar a ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdulllahi Umar Ganduje, inda suka zargi ɓangaren gwamnan da yin babakere a cikin jam’iyyar. Shekarau ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar wadda Manhaja ta samu kwafinta. Cikin sanarwar, Shekarau ya soma ne da miƙa godiya…
Read More
Sanata Shekarau ya koka kan mayar da su saniyar ware a harkokin APC ta Kano

Sanata Shekarau ya koka kan mayar da su saniyar ware a harkokin APC ta Kano

Tsohon gwamnan jihar Kano kuma sanata mai ci, Sanata Ibrahim Shekarau (Sardaunan Kano), ya ce sun shigar da kukansu ga uwar jam'iyyarsu ta APC kan yadda ya ce ana gudanar da harkokin jam'iyyar tasu ba tare da sako su ciki ba. Shekarau ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar wadda Manhaja ta samu kwafinta. Cikin sanarwar, Shekarau ya soma ne da miƙa godiya ga Allah da kuma salati ga Manzon Allah (SAW) albarkacin bikin Maulidi, kana daga bisani ya bayyana halin da ya ce jam'iyyar APC ta Kano ke ciki. A cewarsa, "Ni Sanata Ibrahim Shekarau, na…
Read More
Matawalle ya naɗa kantomomin riƙo a ƙananan hukumomin Zamfara

Matawalle ya naɗa kantomomin riƙo a ƙananan hukumomin Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau  Gwamnan jihar Zamfara Bello Mohammed Matawalle ya rantsar da kantomomin riƙo na ƙananan hukumomi 14 na jihar a ranar Laraba. Da yake jawabi jim kaɗan bayan rantsarwar da aka gudanar a zauren majalisar gidan gwamnatin Gusau, gwamna Matawalle ya umarce su da su ba da fifiko kan yadda za a inganta ɗabi'ar mutane a yankin talakawa musamman kan tsaro da ci gaban ɗan adam. "Don haka dole ne ku yi aiki tuƙuru don tabbatar da amincin da jama'a da gwamnatin jihar Zamfara suka sa muku, sannan kuma ya kamata ku shirya kanku don ayyuka da…
Read More
Cikin wasu ya ɗuri ruwa a Kebbi sakamakon sabuwar dokar fidda gwani

Cikin wasu ya ɗuri ruwa a Kebbi sakamakon sabuwar dokar fidda gwani

Daga JAMIL GULMA a Kebbi Tun lokacin da bayanin majalisar dattawa ta saka hannu a lokacin zaɓen fidda gwani da za a yi labari ya mamaye kafafen yaɗa labarai na cewa cikin wasu ya ɗuri ruwa saboda suna ganin an ruguza duk wani coge da suka kitsa. Sanata Dakta Yahaya Abubakar Abdullahi Mallamawan Kabi Mai wakiltar gundumar Kebbi ta Arewa kuma shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa a wata tattaunawa da ya yi da kafafen yaɗa labarai ya bayyana cewa, majalisar dattawan ta yi haka ne bisa ga la'akari da irin badaƙalar da ake yi wajen tsayar da ‘yan takara…
Read More