Siyasa

INEC ta bayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaɓen Anambara

INEC ta bayyana Soludo a matsayin wanda ya lashe zaɓen Anambara

Daga BASHIR ISAH Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana Farfesa Chukwuma Soludo na jami'iyyar APGA a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Anambara da aka gudanar ran 6 ga Nuwamba. Bayan ƙidayar ƙuri'u, INEC ta ce ƙuri'u 112,229 Soludo ya samu wanda hakan ya ba shi nasara a kan ɗan takar PDP, Mr Valentine Ozigbo wanda ya samu ƙuri'u 53, 807, wato shi ne dan takara na biyu mai mafi yawan ƙuri'u. Sai kuma ɗan takarar APC,Sanata Andy Uba da ya zo na uku da ƙuri'u 43,285. Malamar zaɓen, wato Farfesa Florence Obi, ita ce ta bayyana wannan…
Read More
Zaɓen Anambara: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zaɓe ba

Zaɓen Anambara: Dalilin da yasa ba a bayyana cikakken sakamakon zaɓe ba

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Duk da cewa an tattaro sakamakon zaɓe a ƙananan hukumomi 19 daga cikin 21 na Jihar Anambra, amma har yanzu ba a bayyana sakamakon ƙarshe na zaɓen ba. Masu kaɗa ƙuri'a a faɗin Jihar sun fito ƙwansu da ƙwarkwatarsu a ranar Asabar domin zaɓen gwamnansu na nan gaba. An samu ’yan takara 18 da suka fito neman kujerar a zaɓen, wanda aka dinga samun matsalar na'urar BVAS da aka yi amfani da ita a wasu yankuna. Sai dai, a wurin karɓar sakamakon na ƙarshe a ofishin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa da ke Awka,…
Read More
Zaɓen Anambra bai kammalu ba, inji INEC

Zaɓen Anambra bai kammalu ba, inji INEC

Daga AISHA ASAS Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa zaɓen gwamna da aka yi shekaranjiya da jiya a Jihar Anambra bai kammalu ba, abin da da Turanci ake kira "inconclusive". Hukumar ta ce abin da ya janyo haka shi ne kasa kai ma'aikata da kayan aiki da hukumar ta yi zuwa Ƙaramar Hukumar Ihiala saboda rashin tsaro. Jami'ar kawo sakamakon zaɓe a zaɓen,Farfesa Florence Obi, ita ce ta bayyana haka tare da faɗin cewa za a yi zaɓen a ƙaramar hukumar a ranar Talata, 9 ga Nuwamba. Ya zuwa yanzu dai an bayyana sakamakon zaɓen na ƙananan hukumomi…
Read More
INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zaɓe a wasu rumfuna a zaɓen Anambara

INEC ta tabbatar da batun sace akwatin zaɓe a wasu rumfuna a zaɓen Anambara

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Rahotanni sun bayyana cewa, kwamishinan hukumar zaɓe na INEC a Jihar Anambra, Nwachukwu Orji, ya tabbatar da rahotannin tarzoma da sace-sacen akwatunan zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a Jihar. Ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a gidan Talabijin na Channels a yau Asabar. Orji ya ce, an samu rahotannin sace akwatin zaɓe a wasu rumfunan zaɓe a ƙaramar hukumar Idemili. Hukumar ta ce, ’yan daba sun yi awon gaba da akwatunan zaɓe sama da bakwai ɗauke da ɗaruruwan ƙuri'un zaɓe. A cewarsa, “akwai matsalar sace ƙuri’a a lokacin zaɓen. Wasu ’yan daba ne suka…
Read More
Zaɓen Anambara: Ɗan takarar APGA ya lashe zaɓe a ƙananan hukumomi 11 cikin 21

Zaɓen Anambara: Ɗan takarar APGA ya lashe zaɓe a ƙananan hukumomi 11 cikin 21

Daga MAHDI M. MUHAMMAD Charles Chukwuma Soludo na jam'iyyar APGA ya lashe zaɓen ƙananan hukumomi goma sha ɗaya kawo yanzu da ake cigaba tattara ƙuri'un da aka kaɗa. Ƙananan hukumomin sun haɗa da Awka South, Onitsha South, Orumba South, Anaocha, Anambara East, Njikoka, Orumba North, Aguwata, Oyi, Ayamelum, da Dunukofia. Hukumar zaɓe ta ƙasa INEC ta sanar da cewa za a cigaba da tattara sakamakon zaɓen gobe Lahadi. Akwai ƙananan hukumomi 21 a jihar Anambra, amma sakamakon 11 kaɗai aka sanar. Kawo yanzu, Charles Soludo na da jimillar ƙuri'u 74,859 daga ƙananan hukumomin 11, yayin da ɗan takaran PDP, Valentine…
Read More
Da ɗumi-ɗumi: Yadda ake fafatawa a zaɓen gwamnan Anambara na 2021

Da ɗumi-ɗumi: Yadda ake fafatawa a zaɓen gwamnan Anambara na 2021

An yi gyara a tsarin tsaroBa za a yi zaɓe ba a rumfunan zaɓe 86, inji INECƊan takaran jam'iyyar AAC, Chidozie Nwankwo ya janye daga takarar zaɓen gwamnan AnambaraNa'urar BVAS ta mazaɓar Soludo ta ƙi aikiMasu kaɗa ƙuri'a sun ɓalle da zanga-zanga kan dokar INEC ta hana marasa takunkumi zaɓe Daga MAHDI M. MUHAMMAD Da misalin ƙarfe 8:30 na safiyar yau Asabar ne aka fara kaɗa ƙuri’a a rumfar zaɓen PU005, Umudioka, ƙaramar hukumar Dunukofia da rumfar zaɓe ta Area 13, Ichida 1, ƙaramar hukumar Anaocha ta Jihar Anambara. Kamar yadda muka sani ne cewa, ’yan takara 18 ne suke…
Read More
INEC ta shirya wa zaɓen gwamnan Anambra na ranar Asabar – Yakubu

INEC ta shirya wa zaɓen gwamnan Anambra na ranar Asabar – Yakubu

Daga WAKILINMU Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Anambra cikin lumana wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa, 6 ga Nuwamba. Shugaban hukumar, Farfesa Mahmood Yakubu, shi ne ya bayyana haka a yayin da ya ke ganawa da manema labarai a ranar Talata a ofishin hukumar da ke garin Awka, babban birnin jihar. Ya ce: “Lokacin da hukumar ta saki jadawalin ranakun da za a gudanar da zaɓen, watanni bakwai da su ka gabata, tunanin da wasu su ka yi shi ne lokacin ba zai zo ba.…
Read More
Mun shirya zaɓen Anambra ba gudu ba ja da baya – INEC

Mun shirya zaɓen Anambra ba gudu ba ja da baya – INEC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmoud Yakubu ya bayyana cewa INEC ta shirya tsaf domin gudanar da sahihin zaɓe a ranar 6 ga Nuwamba, 2021 a Jihar Anambra. A ranar 6 ga wata ne za a yi zaɓen gwamnan jihar, a yayin da ake cikin zaman ɗarɗar a jihohin Kudu maso Gabas, musamman a Anambra, inda tsagerun ƙungiyar IPOB su ka yi barazanar hana gudanar da zaɓen. Sun ce ba za su bari a yi zaɓe ba har sai gwamnatin tarayya ta sako masu gogarman su, Nnamdi Kanu wanda ke tsare a…
Read More
PDP ta yi sabbin shugabanni

PDP ta yi sabbin shugabanni

Daga AISHA ASAS Biyo bayan babban taron jam'iyya da suka gudanar a ƙarshen mako, 'ya'yan jam'iyyar PDP sun zaɓi sabbin shugabanni waɗanda za su ci gaba da jan ragamar harkokin jam'iyyarsu nan da wasu shekaru masu zuwa. PDP ta gudanar da babban taron nata a dandalin Eagle Squre da ke Abuja, daga ranar Asabar zuwa wayewan gari safiyar Lahadi. Taron da ya samu hallatar jiga-jigai da kuma ɗimbin magoya bayan jam’iyyar daga sassan ƙasa. Da yake bayyana sakamakon zaɓen, Gwamnan Jihar Adamawa kuma shugaban kwamitin shirya taro, Ahmadu Umaru Fintiri, ya tabbatar da tsohon Shugaban Majalissar Dattawa, Sanata Iyorchia Ayu,…
Read More
Taron PDP: Muna da damar daidaita Nijeriya – Atiku

Taron PDP: Muna da damar daidaita Nijeriya – Atiku

Daga MAHDI M. MUHAMMAD A ranar Asabar ɗin da ta gabata ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar a Abuja ya buƙaci ɗaukacin 'yan Nijeriya da su yi amfani da damar da jam’iyyar PDP ta bayar wajen daidaita Nijeriya da ceto ƙasar daga halin da ta ke ciki. Atiku ya ba da wannan cajin ne ga wakilai da jami'an jam'iyyar a babban taron jam'iyyar PDP na 2021. A cewarsa, akwai bambance-bambance da dama, amma 'yan Nijeriya za su iya cimma komai idan suka ajiye saɓanin da ke tsakaninsu a gefe. Ya ƙara da cewa, taron wata dama ce ta yanke…
Read More