Buhari ya yaba da zaɓukan APC a Katsina

Daga UMAR GARBA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya yaba da yadda aka gudanar da zaɓukan shugabannin jam’iyar APC a Katsina tun daga matakin mazaɓu, ƙananan hukumomi har zuwa matakin jiha.

Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ne ya bayyana haka a lokacin da kwamitin shirya zaɓukan shugabannin jam’iyyar ya miƙa rahotonsa na ƙarshe bayan kammala aikinsa.

Kwamitin wanda ke ƙarƙashin jagorancin shugaban ma’aikatan fadar gidan gwamnati na Katsina, Muntari Lawal da haɗin gwiwa da kwamitin shirya zaɓukan daga uwar jam’iya ta ƙasa.

Masari ya kuma bayyana cewar Shugaba Buhari ya yi matuƙar farin ciki bisa ga yadda aka gudanar da zaɓukan cikin nasara a dukkan jihar.

Yabon da shugaban ƙasar ya yi ya na zuwa ne bayan da aka bayyana ma shi yadda zaɓukan su ka gudana, tun daga shirye-shirye har zuwa kammala zaven, inji Masari.

Gwamnan ya ƙara da cewa an yanke shawarar gudanar da zaɓukan ne ta hanyar masalaha da sasanta ‘yan takara bayan da aka gudanar da wani taron da ya ƙunshi jiga-jigan jam’iyyar na ƙasa da mambobin jam’iyyar dake jihar, inda mafi yawan waɗanda ke riƙe da muƙaman jam’iyyar tun asali suka sake komawa kan kujerunsu, sai dai an canja ma su muƙamai.

A ƙarshen jawabin Gwamna Masari ya gode wa Allah da kuma kwamitocin biyu bisa ga yadda suka gudanar da zaɓukan cikin nasara.

Da yake gabatar da jawabinsa shugaban kwamitin zaɓen a matakin jiha, Alh Muntari Lawal ya ce da taimakon Allah ne suka samu damar kammala aikin su ba tare da fuskantar wata matsala ba.

A jawabin shugaban kwamitin da uwar jam’iyyar ta ƙasa ta turo a Katsina, Hon. Ali Dattuwa Kumo ya yaba wa jam’iyyar APC reshen jihar bisa ga kammala zaɓukan cikin lumana, ya kuma ce a dukkan jihohin da aka gudanar da zaɓukan shugabannin jam’iyyar jihar Katsina ce ta fi yin fice duba da yadda aka gudanar da zaɓukan ba tare da wata hayaniya ba.

Shugabannin jam’iyyar da aka zaɓa sun haɗa da Alh. Muhammad Sani Aliyu a matsayin shugaban jam’iyyar na jiha, sai Alh Bala Abu Musawa a matsayin mataimakin shugaba, sai kuma Alh. Shitu S. Shitu a matsayin sakataren jam’iyyar da dai sauran muƙamai.