Kwalara ta halaka mutane 500 a Jigawa

Daga UMAR AKILU MAJERI a Dutse 

Kimanin mutane 500 cutar Kwalara ta halaka kwanakin baya a yankunan ƙananan hukumomin jihar Jigawa 27. 

Ana sa ran za a yi wa mutane dubu ɗari bakwai allurar rigakafin Kwalara kashi na farko a yankunan ƙananan hukumomin Hadejia, Dutse da ƙaramar hukumar Birnin Kudu da ke jihar ta Jigawa.

Babban sakatare a Hukumar Lafiya Matakin Farko, Dr. Kabir Ibrahim ya ce a ƙaramar hukumar Dutse sun zaɓi ƙauyen Baranda saboda biyayyar su ga shugabannin kuma yanki ne da yake da manyan mutane manoma da albarkatun ƙasa, kuma suna ɗaya daga cikin yankunan da suka yi fama da cutar Kwalara a wancan lokacin.

Ya ce Baranda an zaɓe ta ne daga cikin ƙauyuka dubu goma sha biyu dake faɗin masarautar Dutse a jihar ta Jigawa.

Sakataren ya ce wannan ne karo na farko da aka samar da allurorin rigakafin a jihar Jigawa, kuma ita ce allurar da aka fara yi a faɗin Nijeriya da nufin magance yaɗuwar cutar a doron qasa, an yi nasarar saka jihar Jigawa a cikin jihohin da za su amfana daga rigakafin cutar.

Don haka ya buƙaci jama’ar yankin Baranda da su yi fani da allurar ɗigakafin cutar ta Kwalara, ya ce allurar tana da matuƙar muhimmanci ga al’umma.

Shi ma da yake nasa jawabin, Mai martaba Sarkin Dutse Alhaji Nuhu Muhammed Sunusi ya ce maƙasudin bada rigakafin cutar ta ciwon Kwalara shi ne sakamakon mace-macen da ya faru a kwanan baya, ita kuma faruwar cutar ta faru ne sakamakon ƙazanta da rashin tsaftar muhalli da jama’a ba sa iya lura da shi.

Sarkin ya ƙara da cewar mutanen Baranda sun yi matuƙar sa’a da suka samu kansu cikin mutanen da aka zaɓa domin amfana da allurar rigakafin a faɗin Nijeriya karo na farko.

Sarkin ya tabbatar da ingancin allurar cewar tana da kyau sosai, saboda haka ya buƙaci mutane su amshi allurar hannu biyu-biyu. Sarkin ya kuma ɗigawa wasu jami’an gwamnati allurar a gaban jama’a, kuuma shi ma ya sha domin jam’a su tabbatar da cewar allurar tana da kyau ba ta da wata illa a rayuwar su.

Da yake jawabin godiya, Dagacin Baranda Malam Idris Abdulmumini ya gode wa masarautar Dutse da gwamnatin jihar Jigawa saboda irin kulawar da ake ba su ta fuskar kiwon lafiya, ya ce dukkan agajin da suke samu suna samu ne da taimakon masarautarsa.

Ya kuma yi kukan yankin suna fama da matsalar zaizayar ƙasa, don haka ya buƙaci gwamnatin jihar Jigawa da ta kawo masu ɗauki domin ceto su daga matsalar.

Ya kuma buqaci gwamnatin jihar da ta faɗaɗa aikin noma a yankin ta gina masu madatsar ruwa da nufin inganta harkokin noman damina da na rani.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *