22
Mar
Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya karɓi bakuncin tsohon Shugaban Majalisar Wakilai, Mr Dimeji Bankole da tsohonn Gwamnan Jihar Ogun, Mr Gbenga Daniel a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja bayan da suka sauya sheƙa zuwa jam'iyyar APC. Tawagar ta ziyarci Fadar Shugaban ƙasar ne ƙarƙashin jagoranci Shugaban Kwamitin Riƙo na APC kuma gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni tare da Gwamna Abubakar Atiku Bagudu na jihar Kebbi da kuma Gwamna Mohammed Badaru na Jigawa. Da yake amsa tambayoyin manema labarai jim kaɗan bayan kammala ganawarsu, Mai Mala Buni ya ce Shugaba Buhari ya yi matuƙar farin ciki…
