13
Feb
Daga AISHA ASAS Gwamnatin Jihar Kano ta rantsar da sabbin zaɓaɓɓun shugabannin ƙananan hukumomin jihar su 44 a Juma'ar da ta gabata. Sa'ilin da yake jawabi yayin bikin rantsarwar, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya ce cika aiki shi ne babban abin da gwamnatinsa ta fi maida hankali a kai. Tare da kira a gare su da su kasance masu ƙwazo da kuma yin aiki da gaskiya. A cewar gwamnan, ƙanan hukumomi a matsayin mataki na uku na tsarin gwamnati na buƙatar jajirtattun shugabanni da za su yi aiki tukuru. Yana mai cewa sadaukarwa da kuma cika aiki su ne…
