Siyasa

Wike ya gargaɗi gwamnoni su daina tsoma baki a harkokin PDP a Ribas

Wike ya gargaɗi gwamnoni su daina tsoma baki a harkokin PDP a Ribas

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, ya sha alwashin haifar da rikicin siyasa a jihar, ya kuma gargaɗi duk wani gwamna aka da ka da ya yi yunƙurin yin katsalandan a harkokin jam’iyyar PDP a jihar Ribas. Wike ya bayyana haka ne a sakatariyar jam’iyyar PDP da ke Fatakwal a ranar Asabar a yayin taron jam’iyyar na jihar. “Bari na tabbatar muku, ba yayin da muke raye ba wani zai ƙwace mana tsarin PDP. Amma bari in gaya wa mutane, na ji wasu gwamnonin suna cewa za su karɓe tsarin su mayar wa wani,…
Read More
APC shiyyar Arewa ta Tsakiya ta yi Allah wadai da Gwamna Sule kan amincewa da Ganduje

APC shiyyar Arewa ta Tsakiya ta yi Allah wadai da Gwamna Sule kan amincewa da Ganduje

Daga SANI AHMAD GWA a Abuja Kungiyar Gwamnonin APC ta Arewa ta Tsakiya ta yi Allah wadai da amincewa da Shugaban Jam’iyyar na ƙasa Abdullahi Ganduje da shugaban ƙungiyar gwamnonin Arewa ta tsakiya kuma gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya yi. Da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar taron da ke Jos babban birnin Jihar Filato, Shugaban ƙungiyar, Alhaji Saleh Zazzaga, ya ce ziyarar ban girma da Sule ya kai wa sakatariyar jam’iyyar a Abuja ranar Juma’a domin ya nuna goyon bayan Ganduje don son kai da son rai ba wll ba wai muradin yankin Arewa ta tsakiya ba,…
Read More
Babu wani mutum da zai rusa mana jam’iyya, PDP ta ƙalubalanci Wike

Babu wani mutum da zai rusa mana jam’iyya, PDP ta ƙalubalanci Wike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP sun ƙalubalanci tsohon gwamnan jihar Ribas kuma ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da cewa ba zai iya ruguza jam’iyyar ba. Wike, yayin da yake magana a sakatariyar jam’iyyar PDP a Fatakwal, babban birnin jihar Ribas, a ranar Asabar a yayin taron jam’iyyar na jihar, ya gargaɗi gwamnonin PDP da su daina shiga al’amuran jam’iyyar a Ribas, inda ya yi barazanar sanya wuta a jihohinsu. Ya ci gaba da cewa, “Bari na tabbatar muku da cewa, ba yayin da muke raye babu wanda zai ƙwace mana tsarin jam’iyyar PDP. Amma…
Read More
Gwamnonin PDP na son jami’an tsaro su ɗauki mataki kan ‘barazanar’ da Wike ya yi musu

Gwamnonin PDP na son jami’an tsaro su ɗauki mataki kan ‘barazanar’ da Wike ya yi musu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ƙungiyar gwamnonin jam'iyyar PDP ta buƙaci jami'an tsaron Nijeriya su ɗauki mataki kan 'barazanar' da suka ce Ministan Abuja, Nyesom Wike ya yi musu. A ƙarshen makon a ya gabata ne dai tsohon gwamnan na jihar Ribas ya yi barazanar haifar da rikicin siyasa a jihohin gwamnonin jam'iyyar, matsawar suka ci gaba da sa baki kan rikicin siyasar jihar Ribas. ''Na ji wasu gwamnoni da suka ce za su ƙwace jam'iyyarmu don miƙa wa wani, Ina tausaya wa waɗannan gwamnoni, saboda zan kunno musu wutar da ba za su iya kashe ta ba a…
Read More
Domin kyautata cigaban al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa na fito takara – Hon. Bomboy

Domin kyautata cigaban al’ummar ƙaramar hukumar Nasarawa na fito takara – Hon. Bomboy

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Honorabul Muhammed Adamu Bomboy ya ce ya  fito neman takarar kujerar Shugaban ƙaramar Hukumar Nasarawa ne domin kawo cigaba a yankin idan aka yi la'akari da yadda ta zama koma  baya a wasu ɓangarori na bunƙasa cigaban rayuwar al'ummarta. Hon. Mohammed adamu (Bomboy) Gama ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida akan neman takarar shugabancin ƙaramar hukumar Nasarawa da ya fito. Ya ce ita dama manufar dimukraɗiyya don matso da gwamnati kusa da mutane  ne,musamman a ƙaramar hukuma amma sai gashi ana samun rauni akan haka daga wasu da suka riƙe ƙaramar…
Read More
APC ta lashe zaɓukan ciyamomi 21 da kansiloli gabaɗaya a Kebbi

APC ta lashe zaɓukan ciyamomi 21 da kansiloli gabaɗaya a Kebbi

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kebbi a ranar Lahadi, ta bayyana jam’iyyar All Progressives Congress(APC) a matsayin wadda ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar a jihar. Shugaban Hukumar, Aliyu Muhammad-Mera, wanda ya bayyana hakan a Birnin Kebbi ranar Lahadi, ya ce jam’iyyar ta lashe dukkan kujerun Shugabanci 21 da Kansiloli 225. Muhammad-Mera ya ce jam’iyyun siyasa 17 ne suka shiga zaɓen da suka haɗa da, APC, NNPP, LP, AAC, Boot party, AP, SDP da dai sauransu. Sai dai jam'iyyar PDP ta fice daga zaɓen in da tai zargin cewa shugabannin hukumar zaɓen jihar…
Read More
Lalube cikin duhu gwamnatin Tinubu take yi —Atiku

Lalube cikin duhu gwamnatin Tinubu take yi —Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce yanayin Gwamantin Tinubu daidai yake da mota a tsakiyar jeji babu direba. Atiku ya bayyana gwamtin a matsayin mara alƙibla ce a yayin da yake sukan sabon tsarin da ta ɓullo da shi na haramta wa ɗalibai 'yan ƙasa da shekaru 18 zana jarabawar kammala sakandare. Dokar, “ta fito fili da ɗabi’ar Gwamnatin Tinubu, wadda take daidai da matuƙin jirin ruwan da ya ɓace a tsakiyar teku,” inji shi. A martanin da ya wallafa ranar Laraba a shafinsa na ɗ, Atiku ya ce dokar ba komai…
Read More
Jigo a APC, George Moghalu ya fice daga jam’iyyar

Jigo a APC, George Moghalu ya fice daga jam’iyyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar All Progressiɓes Congress (APC) ta gamu da babban koma-baya a jihar Anambra yayin da tsohon manajan darakta na hukumar kula da hanyoyin ruwa ta ƙasa (NIWA) kuma wanda aka kafa jam’iyyar da shi, Cif George Moghalu ya fice daga jam’iyyar. Tsohon mai binciken kuɗi na jam’iyyar APC na ƙasa, a wata takarda da ya miƙa takardar ficewa daga jam’iyyar, mai ɗauke da kwanan wata 26 ga watan Agusta, 2024, ya aika wa shugaban jam’iyyar Uruagu Ward 1 na jam’iyyar APC a Nnewi, ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa a jihar Anambra, ya ce:  “Ina…
Read More
Ina sukar Tinubu ba don na tsane shi ba — Jigo a NNPP

Ina sukar Tinubu ba don na tsane shi ba — Jigo a NNPP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jigo a Jam’iyyar NNPP, Ambasada Olufemi Ajadi, ya bayyana cewa duk wata suka da yake yi wa mulkin Shugaba Bola Tinubu, yana yin ne domin taimaka masa don yin nasara. Ajadi, yayin da yake amsa tambayoyin ‘yan jarida, ya musanta maganganun da ke cewa ya saba sukar Gwamnatin Tarayya da jam’iyyar APC saboda ƙiyayya ga Shugaban ƙasa. Ya jaddada cewa, a matsayinsa na cikakken ɗan ƙabilar Yarbawa, ba shi da wani dalili da zai yi ƙiyayya ga ɗaya daga cikin shugabanninsu. Ya bayyana cewa “A al’adun Yarbawa haramun ne a ƙi ɗan uwa ko…
Read More
Yadda Magaji Ɗanbatta ya taimaki takarata a 2003 — Shekarau

Yadda Magaji Ɗanbatta ya taimaki takarata a 2003 — Shekarau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana yadda ya sha wahala wajen samun Naira miliyan biyar da ake buƙata domin sayan fom ɗin takarar gwamna a zaɓen 2003. Abokansa da wasu ’yan siyasa sun tara masa Naira miliyan 1.5, amma hakan bai wadatar domin sayan fom ɗin takarar ba. Shekarau, ya bayyana yadda ya nemi taimakon marigayi Malam Magaji Danbatta, wanda a lokacin shi ne shugaban ƙungiyar masu rajin kare Kano. ɗanbatta ya amince ya ba shi bashin Naira miliyan ɗaya domin cika kuɗin da yake nema don sayan fom ɗin takarar…
Read More