Siyasa

Kotu ta yi watsi da buƙatar APC ta hana zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Kotu ta yi watsi da buƙatar APC ta hana zaɓen ƙananan hukumomin Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ƙi amincewa da buƙatar da jam’iyyar APC ta shigar na neman hana hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Kano, KANSIEC gudanar da zaɓen ƙananan hukumomin jihar da za a yi a ranar 26 ga watan Oktoba. Masu ƙarar su ne Aminu Aliyu Tiga da jam’iyyar APC ta hannun lauyansa, Mustapha Idris, inda su ka shigar da ƙara a ranar 18 ga watan Satumba tare da miƙa ƙorafin a ranar 20 ga watan Satumba. Su na neman kotu da ta hana KANSIEC gudanar da…
Read More
Kotu ta hana jam’iyyu 19 shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

Kotu ta hana jam’iyyu 19 shiga zaɓen shugabannin ƙananan hukumomi a Kano

Daga USMAN KAROFI Babbar kotu a Jihar Kano wanda mai shari'a Sanusi Ado Ma'aji ke jagoranta ta dakatar da aƙalla jam'iyyun siyasa 19 daga shiga zaɓen ƙananan hukumomi a jihar. Umarnin koton kamar yadda hukumar zaɓe ta jihar ta buƙata shine hana jam'iyyun yin katsalandan a zaɓen a ƙananan hukumomi 44 da ke faɗin kano. Mai ƙara itace hukumar zaɓe mai zaman kanta ta Jihar Kano. Sai kuma waɗanda ake ƙara sun haɗa da jam'iyyu kamar su , People Democratic Party (PDP), Accord Party( AP), All Progressive Congress ( APC) da sauran su. Alƙalin ya ɗage shari'ar zuwa 10 ga…
Read More
PDP ta koka kan zargin katsalandan a tattara sakamakon zaɓen Edo

PDP ta koka kan zargin katsalandan a tattara sakamakon zaɓen Edo

Shugaban yaƙin neman zaɓen Gwamnan Jihar Edo, kuma Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umar Fintiri, na jam’iyyar PDP, ya fitar da sakamakon da ya samu a zaɓen da aka gudanar a ranar Asabar. Fintiri wanda ya karanta wa ‘yan jarida sakamakon a wani taron manema labarai a birnin Benin, ya ce; "Duk wani abu da za ayi bayan wannan zai kasance ba bisa ƙa'ida ba, ya zama cin zarafi ne da son rai da cin mutuncin dokar zaɓe ta 2022." Gwamna Godwin Obaseki (Edo) Sheriff Oboriworhe (Delta) da Agbu Kefas (Taraba), sun kasance tare a daidai lokacin da yake ya ke…
Read More
Ba zan sake goyon bayan Fubara ba har abada – Wike

Ba zan sake goyon bayan Fubara ba har abada – Wike

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Babban Birnin Tarayya, FCT Abuja Nyesom Wike, ya ce sha alwashin cewa ba zai sake goyon bayan Gwamna Fubara na Jihar Ribas ba, har abada. Wike wanda tsohon gwamnan jihar Ribas ne wanda shi ya gama wa’adinsa Fubara ya maye gurbinsa, ya ce har abada babu sauran shiri ko sasanci tsakaninsa da Fubara. “Ba zan taɓa sake goyon bayan Fubara ba a tafiyar siyasa, har ƙarshen rayuwa ta. Ba wai don Ni ba. Mutane sun sha wahala sun gina jam’iyya bisa tafiya mai tsari, amma wahalar ta zama ta banza,” haka Wike ya…
Read More
Gwamnan Bauchi ga Wike: Babu wanda zai iya rura wutar rikici a jiha ta

Gwamnan Bauchi ga Wike: Babu wanda zai iya rura wutar rikici a jiha ta

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya ce babu wanda zai iya kunna wuta a Bauchi "saboda muna da adadin ruwan da za mu iya kashe wutar". Ya bayyana haka ne a lokacin da ya karbi baƙuncin tawagar kwamitin ayyuka na ƙasa (NWC) na jam’iyyar PDP a ranar Talata. Ya ce, “Muna tare; babu wanda zai iya saka wuta a Bauchi. Muna da ruwa mai yawa wanda zai kashe wutar, har abokina da ya ce ya yi haka saboda yana jin haushi. Watakila na faɗi wani abu da ya ɓata masa rai amma ba…
Read More
Na gamsu da zaɓin Ogan ɓoye a matsayin ɗan takarar ciyaman na ƙaramar Hukumar Nasarawa – Zannan Kwankwasiyya 

Na gamsu da zaɓin Ogan ɓoye a matsayin ɗan takarar ciyaman na ƙaramar Hukumar Nasarawa – Zannan Kwankwasiyya 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Zannan Kwankwasiyya, jigo a Jam'iyyar NNPP, tsohon babban mataimaki na musamman ga Gwamnan jihar Kano Abba Kabir Yusuf akan kasuwanci da cigaban masana'antu, ya bayyana gamsuwa da zaɓin da aka yi wa Hon. Yusuf Imam da aka fi sani da Ogan ɓoye a matsayin ɗan takarar shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa. Ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai inda ya faɗi a matsayinsa na ɗaya daga cikin waɗanda suka nemi takarar ya ce kamar yadda ya faɗa a baya cewa duk lokacinsa aka yi hukunci za su yi maraba da hukuncin kuma Allah ya…
Read More
Ribaɗu ya yi barazanar shiga kotu da ɗan takarar Edo na PDP

Ribaɗu ya yi barazanar shiga kotu da ɗan takarar Edo na PDP

Mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, ya buƙaci shugaban PDP na Jihar Edo Anthony Aziegbemi ya janye zargin ya yi masa kan zaɓen gwamna da za a yi a jihar. Aziegbemi dai ya zargi gwamnatin tarayya da shirin yin magudi a zaɓen, inda ya ce Malam Ribadu ya bayar da dala miliyan biyu ga ɗan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaɓen. A cikin takardar ranar 15 ga Satumba, 2024, lauyoyin Malam Ribadu, Charles Musa & Co, sun bayyana zargin a matsayin "ƙarya ce kwata-kwata" kuma sun buƙaci a janye shi cikin gaggawa. Lauyoyin sun bayyana…
Read More
Taron Sanata Barau: Jami’an tsaro sun lakaɗa wa wani masoyinsa duka           

Taron Sanata Barau: Jami’an tsaro sun lakaɗa wa wani masoyinsa duka           

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano   Hon. Ibrahim Iliyasu, shugaban ƙungiyar wayar da kai ta siyasar matasa masoyan Sanata Barau I Jibirin da ake kira Mai Kaza Political Awarness, ya koka da roƙon DSP Barau da ya tsawatarwa jami'an tsaronsa kan yadda suke tozarta jama'a a duk wani taro na DSP kamar dai yadda ya zargi jami'an tsaron Sanata Barau sun yi masa dukan tsiya ta hanyar cakumosa a daidai lokacin da yake sauraron jawabin Sanata a ɗakin taron Ammani da aka yi a makon nan a Kano, inda suka yi masa duka bai san abin da ya musu ba. Hakan…
Read More
Muna matuƙar jin daɗi da alfahari da wakilcin ɗan majalisar tarayya na Gwale – Dakta Sani Shehu

Muna matuƙar jin daɗi da alfahari da wakilcin ɗan majalisar tarayya na Gwale – Dakta Sani Shehu

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana ɗan majalisar tarayya mai wakiltar ƙaramar Hukumar Gwale, Hon. Garba Ibrahim ɗiso da cewa jajirtaccen wakili ne da yake kyakkyawan wakilci ga al'ummarsa. Dakta Gaddafi Sani Shehu mataimakin Manajan Daraktan KHEDCO, sakataren yaƙin neman zaɓen Garba Diso ne a 2023  ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida. Ya ce a kowane lokaci ɗan majalisar na cuɗanya da al'ummar da jin buƙatunsu da tallafawa matsalolinsu da kawo aikace-aikace ta ɓangarori daban-daban duk da cewa aikin ɗan majalisa na yin doka ne amma yana ƙoƙarin yin ayyuka. Ya ce suna alfahari da ɗan…
Read More
2027: Atiku, Kwankwaso da Obi na tattaunawar yin maja, inji PDP

2027: Atiku, Kwankwaso da Obi na tattaunawar yin maja, inji PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Manyan ‘yan adawa uku a Nijeriya na tattaunawa kan yuwuwar haɗaka domin goyon bayan ɗan takara don fafatawa da jam'iyyar APC da fitar da ‘yan Nijeriya daga yunwa da taɓarɓarewar tsaro gabanin zaɓen Shugaban ƙasa na 2027, in ji kakakin jam’iyyar PDP a ranar Litinin. Mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na ƙasa Ibrahim Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin shirin Sunrise Daily na gidan talabijin na Channels a ranar Litinin da News Point Nigeria ke sa ido. Ya ce ‘yan takarar jam’iyyar adawa uku a zaɓen da ya gabata – Atiku Abubakar na PDP,…
Read More