Siyasa

Tsagin jam’iyyar PDP sun naɗa Yayari Ahmed a matsayin shugaban riƙon ƙwarya

Tsagin jam’iyyar PDP sun naɗa Yayari Ahmed a matsayin shugaban riƙon ƙwarya

Jam'iyyar PDP ta naɗa Ahmed Yayari wanda shine ma'ajin jam'iyyar a matsayin sabon shugaban ta na riƙon ƙwarya bayan dakatar da Umar Damagun da wani tsagin kwamitin gudnarwar jam'iyyar ya yi. Sanarwa ta fito a wata takarda wadda sakataren jam'iyyar Hon. Debo Ologunagba ya sanya wa hannu a ranar Juma’a a Abuja. Sanarwar ta bayyana Yayari Ahmed a matsayin sabon shugaban riƙon ƙwarya kamar yadda kundin tsarin mulkin jam'iyyar ya bada damar yin hakan. Kwamitin ya roƙi mambobi da su haɗe kansu kuma su maida hankali ga taron kwamitin gudanarwa da ake sa ran za ayi 24 ga watan Oktoba…
Read More
Atiku ya yaba wa mutanen Ribas da Fubara kan yadda suka bijire wa barazana

Atiku ya yaba wa mutanen Ribas da Fubara kan yadda suka bijire wa barazana

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ya yabawa mutanen Jihar Ribas da gwamna Similaye Fubara bisa jajircewa da kuma bijire wa tsangwama a zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka gudanar ranar Asabar. Atikun yayi wannan jawabin ne a shafin sada zumunta na X. Ya bayyana gamsuwarsa da yanayin yadda aka gudanar da zaɓen. Yayi matuƙar farin ciki da kyara da tsangwama bai hana mutane fitowa su yi zaɓe ba. Ya ƙara yabawa da irin jajircewa da mutanen Ribas su ka yi na ganin zalunci da siyasar uban gida bai yi tasiri ba. Daga ƙarshe ya sake yabawa gwamna Fubara yadda…
Read More
Nijeriya na neman hawa tsarin kama-karya na jam’iyya ɗaya – Atiku

Nijeriya na neman hawa tsarin kama-karya na jam’iyya ɗaya – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A yayin da Nijeriya ke bikin cika shekaru 64 da samun 'yancin kai, tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar yayi kira da manyan 'yan siyasa su haɗa kansu don kare dimukuraɗiyyar ƙasar daga hawa kan tsarin kama karya. Atiku, a wata sanarwa da ya sanyawa hannu da kansa, ya ambato cewa fannin siyasa na samun cikas a sannu a hankali a ƙasar nan a yayin da jam'iyyun adawa ke ƙara samun rauni a daidai lokacin da jam'iyya mai mulki ke haddasa wutar rikici a jam'iyyun don hana su tasiri. ɗan takarar shugaban ƙasar na…
Read More
Ubangiji ya ce kada in tsaya takara a 2027 – Ortom

Ubangiji ya ce kada in tsaya takara a 2027 – Ortom

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya ce Allah ya ce kada ya tsaya takara a 2027. Mista Ortom ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Makurdi lokacin da mambobin jam’iyyar People’s Democracy Party, PDP, G-14 suka kai masa ziyarar ban girma. Mambobin G-14 dattawan jam’iyyar PDP ne a ƙananan hukumomi 14 da ke magana da harshen Tibi a Benue. Tsohon gwamnan ya ce ba shi da wani zaɓi illa mutunta nufin Allah. Ya yarda cewa ya kasa tuntuɓar Allah kafin ya shiga zaɓen 2023, shi ya sa ya sha kaye. Mista Ortom…
Read More
PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Anambra

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin Anambra

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar PDP reshen Anambra ta yi watsi da sakamakon zaɓen ƙananan hukumomin jihar da aka yi ranar Asabar. Cif Chigozie Igwe, shugaban jam'iyyar PDP a Anambra ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya a Awka a ranar Litinin. Geneɓieɓe Osakwe, Shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Anambra, ANSIEC, a daren Lahadin da ta gabata, ta bayyana ’yan takarar ciyamomi da kansiloli na jam’iyyar All Progressiɓe Grand Alliance, APGA, a matsayin waɗanda suka lashe zaɓen ƙananan hukumomi 21 da kuma gundumomi 326. Osakwe a lokacin da yake bayyana…
Read More
Da Ɗumi-Ɗumi: APP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi 22 cikin 23 a Jihar Ribas

Da Ɗumi-Ɗumi: APP ta lashe zaɓen ƙananan hukumomi 22 cikin 23 a Jihar Ribas

Jam’iyyar Action People’s Party (APP) ta lashe kujeru 22 daga cikin 23 a zaɓen ƙananan hukumomi da aka kammala a Jihar Ribas. Babban Jami’in Zabe na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Jihar Ribas, Mai Shari’a Adolphus Enebeli ne ya bayyana sakamakon zaɓen ranar Asabar a Fatakwal. Ya ce an dakatar da sanarwar ne a karamar hukumar Etche saboda har yanzu ana ci gaba da tattara sakamakon zaɓen. Sauran bayanai na zuwa...
Read More
Tafiyar Kwankwasiyya na daf da rushewa – Sanata Barau

Tafiyar Kwankwasiyya na daf da rushewa – Sanata Barau

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana a Abuja ranar Juma’a cewa rushewar tafiyar Kwankwasiyya na nan tafe a Kano, domin zai yi wuya a ga wani yana sanye da jar hula nan ba da jimawa ba. Barau ya yi wannan bayani a ofishinsa lokacin da ya karɓi ɗaruruwan mambobin jam’iyyar NNPP da suka koma jam’iyyar APC. A cewarsa, yadda ‘yan NNPP, ciki har da shugabanninsu, ke tururuwar shigowa APC, shaida ce ga ƙaruwar farin jinin da APC ke samu a Jihar Kano duk da kasancewarta jam’iyyar adawa a jihar.Ya ce, “Zan ci gaba da karɓar ‘yan NNPP…
Read More
Rikicin PDP ya ƙara ta’azzara bayan da Atiku ya goyi bayan tsige Damagum

Rikicin PDP ya ƙara ta’azzara bayan da Atiku ya goyi bayan tsige Damagum

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar ya goyi bayan shirin tsige muƙaddashin shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum. Bayanai sun nuna cewa Atiku ya fara tuntuɓar 'yan kwamitin gudanarwa (NWC) waɗanda suka fara fafutukar sauke Damagum daga shugabancin jam’iyyar. Jaridar Punch ta tattaro cewa shirin tsige Umar Damagum ya raba kawunan gwamnoni 13 na jam’iyyar adawa PDP. Gwamnoni bakwai ƙarƙashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed na Bauchi sun haɗa kai, sun matsala lamba kan dole Damgum ya bar muƙaminsa. Yayin da gwamnoni huɗu ƙarƙashin Gwamna Seyi Makinde na Oyo suka nuna gamsuwa da…
Read More
PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Edo, za ta garzaya kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar PDP ta yi watsi da sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Edo, tare da bayyana ƙudirinta na garzayawa kotu don ƙalubalantar sakamakon. A wani taron manema labarai da ta gudanar a Abuja, Shugaban riƙo ƙwarya na jam’iyyar PDP, Ambasada Umar Damagum, ya buƙaci Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC), da ta sake duba sakamakon zaɓen. Ya ce ya kamata INEC ta sanar da sakamakon gaskiya da ya fito daga ƙuri’un da jama’ar jihar suka kaɗa a rumfunan zaɓe. Damagum, ya yi iƙirarin cewa mutanen Edo sun zaɓi ɗan takararsu, Dokra Asue Ighodalo, amma…
Read More
Nasarar APC a Edo ya tabbatar ‘yan Nijeriya sun yi na’am da salon mulkin Tinubu – Sanata Barau

Nasarar APC a Edo ya tabbatar ‘yan Nijeriya sun yi na’am da salon mulkin Tinubu – Sanata Barau

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa nasarar da jam’iyyar APC ta samu a zaɓen Edo nuni ne cewa tabbas 'yan Nijeriya sun yi na’am da mulkin shugaba Bila Tinubu. Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta ƙasa (INEC) bayyana Okpebolo, ɗan takarar jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna na Edo. Okpebholo ya samu ƙuri’u 291,667 inda ya doke abokin hamayyarsa kuma ɗan takarar jam’iyyar PDP, Asue Ighodalo, da ya samu ƙuri’u 247,274. Dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP), Olumude Akpata, ya zo na uku da ƙuri’u 22,763, yayin da sauran ‘yan takara…
Read More