03
Nov
Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano A jihar Kano, har yanzu tsugune ba ta ƙare ba, duk da kammala zaɓen ƙananan hukumomi tare da rantsar da sabbin shugabannin, saboda rikicin shari’a. Hukumar zaɓen Kano ta ce jam’iyyar NNPP ce ta lashe duk shugannin ƙananan hukumomi 44 da kansiloli 484, to sai dai har yanzu ba a rantsar da shugaban ƙaramar hukumar Kumbotso ba. Daya daga cikin 'yan takarar kujerar ne ya garzaya babbar kotun jihar saboda sauya sunansa da wani, abin da ya sa kotu ta yi hukuncin da ake ganin shi ne ya hana rantsar da sabon shugaban. Ana gobe…
