17
Nov
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sabon ƙaramin Ministan Gidaje da Raya Birane, Yusuf Abdullahi, ya sha alwashin tabbatar da nasarar jam’iyyar APC a zaɓen 2027. Ministan na wannan kalamai ne a yayin ganawarsa da manema labarai bayan dawowarsa Kano daga Abuja a ranar Lahadi. Ya yi alƙawarin jajircewa wajen yayata ayyukan da shugaba Tinubu ke yi na sabunta fatan ‘yan Nijeriya. Sannan ya jaddada aniyarsa ta cicciɓa aikin samar da gidajen da gwamnatin shugaba Tinubu ke yi tare da gode wa shugaban bisa karrama shi da wannan muƙami da ya yi. Ministan ya yi alƙawarin tabbatar da nasarar jami’iyyar…
