Siyasa

Kansiloli sun tsige Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma a Katsina

Kansiloli sun tsige Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukuma a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Kansilolin Ƙaramar Hukumar Malumfashi guda 9 cikin 12 sun gudanar da wani zama na musamman tare da tsige Shugaban Majalisar, Hon. Abdullahi Rabi'u mai wakiltar mazaɓar Yaba da mataimakin shi, Hon Mustapha Ma'azu mai wakiltar mazaɓar Gorar-Dansaka. Haka zalika kamar yadda ɗaya daga cikin kansilolin ya shaida wa Blueprint Manhaja, kansiloli sun kuma tsige Mataimakin Shugaban Ƙaramar Hukumar ta Malumfashi, Hon Abdulrazak Tukur Maifada bisa zarge-zargen aikata ba daidai ba. Daga bisani kansilolin sun naɗa sababbin shuwagabannin kamar haka:- Hon. Salmanu Saminu a matsayin Shugaban Majalisar; Hon. Ibrahim Muhammed Rahimi (Yammama Ward) a matsayin Mataimakin…
Read More
Zaɓen Adamawa: IGP ya canja Kwamishinan ‘Yan Sanda mai lura da zaɓen jihar

Zaɓen Adamawa: IGP ya canja Kwamishinan ‘Yan Sanda mai lura da zaɓen jihar

Babban Sufeton 'Yan Sanda (IGP), Usman Baba, ya ba da umarnin janye Kwamishinan 'Yan Sanda mai lura da sha'anin zaɓe a Jihar Adamawa, Mohammed Barde. Manhaja ta gano cewar IGP ya sake ba da umarnin gaggawa a kan Kwamishinan 'Yan Sanda mai kula da Jihar Gombe, CP Etim Equa, ya koma Adamawa da aiki don ci gaba da lura da sha'anin zaɓen gwamnan jihar wanda bai kammala ba. Da yake zantawa da manema labarai ranar Talata a Abuja, Kakakin Rundunar 'Yan Sanda, Muyiwa Adejobi, ya ce IGP na bakin ƙoƙarinsa wajen tabbatar da komai ya gudana cikin nasara. A cewarsa,…
Read More
Shugabancin Adamawa: Fintiri ya zarce

Shugabancin Adamawa: Fintiri ya zarce

Hukumar Zaɓe ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na Jam'iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamna a Jihar Adamawa. Sakamakon zaɓe ya nuna Fintiri ya lashe zaɓen cike giɓin da ya gudana a jihar Asabar da ta gabata da ƙuri'u 9,337 wanda hakan ya ba shi damar doke abokiyar hamayyarsa ta Jam'iyyar APC, Sanata Aishatu ‘Binani’ Dahiru wadda ta tsira da ƙuri'u 6,513. Bayan kammala zaɓen baki ɗaya, alƙaluma sun nuna Fintiri ya tashi da ƙuri'u 430,861, yayin da Binani ta samu ƙuri'u 398,788. Da yammacin ranar Talata INEC ta kawo ƙarshen tirka-tirkar zaɓen na gwamnan Adamamwa inda ta…
Read More
INEC ta tsayar da ranar bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Adamawa

INEC ta tsayar da ranar bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Adamawa

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta tsayar da ranar da za ta bayyana sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Adamawa. Ya zuwa ranar Alhamis ake sa ran INEC ta bayya sakamakon zaɓen na Adamawa. A cewar Kwamishina a hukumar, Dr Festus Okoye, INEC za ta yi zama a ranakun Talata da Laraba don tattauna batun. A ranar Litinin INEC ta dakatar da Kwamishinan Zaɓe na Jihar Adamawa (REC), Hudu Yunusa Ari, saboda riga-malam-masallacin da ya yi wajen karɓe ikon Baturen Zaɓe tare da bayyana 'yar takarar Jam'iyyar APC, Sanata Aisha Dahiru Binani, a matsayin wadda ta lashe zaɓe tun kafin kammala tattara…
Read More
Sanata Marafa ya amince da shan kaye, ya ce babu batun zuwa kotu

Sanata Marafa ya amince da shan kaye, ya ce babu batun zuwa kotu

Ɗan takarar Sanatan Zamfara ta Tsakiya ƙarƙashin Jam'iyyar APC, Sanata Kabiru Garba Marafa, ya ce ya amince ya sha kaye a hannun takwaransa na PDP, Hon. Ikira Aliyu Bilbis. A jawabinsa da aka yaɗa ranar Litinin, Marafa ya yi alƙawarin ba zai tafi kotu don ƙalubalantar sakamakon zaɓen ba. Saboda a cewarsa, zuwa kotu zai karkatar da hankalin zaɓaɓɓen sanatan daga barin yin aikin da ya kamata, wanda hakan kuwa zai shafi shiyyarsu. Ɗan siyasar ya yi amfani da wannan dama wajen yaba wa al'ummar Zamfara ta Tsakiya dangane da damar da suka ba shi ta zame musu wakili a…
Read More
Sanata Binani ta garzaya kotu neman adalci

Sanata Binani ta garzaya kotu neman adalci

'Yar takarar gwamna ta Jam'iyyar APC a Jihar Adamawa, Sanata Aisha Binani Dahiru, ta garzaya kotu don neman a yi mata adalci a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamna a jihar. Aisha ta tafi Babbar Kotu a Abuja ne inda ta shigar da ƙarar neman kotu ta dakatar da matakin da Hukumar Zaɓe, INEC, ta ɗauka na soke bayyana ta a matsayin wadda ta lashe zaɓen Gwamnan Adamawa bayan zaɓen da ya gudana ranar 18 ga Maris wanda aka kammala ran 15 ga Afrilu. Kazalika, Sanata Binani na neman kotu ta hana INEC ɗaukar wani mataki na gaba dangane da…
Read More
Nasiru Idris ya zama Gwamna mai jiran gado a Kebbi

Nasiru Idris ya zama Gwamna mai jiran gado a Kebbi

Ɗan takarar gwamna na Jam'iyyar APC a Jihar Kebbi, Nasiru Idris, ya zama sabon zaɓaɓɓen Gwamnan jihar. A ranar Lahadi INEC ta bayyana Idris a matsayin wanda ya lashen zaɓen gwamnan jihar bayan kammala zaɓen gwamnan jihar a ranar Asabar da ta gabata. Ya lashe zaɓen ne bayan da ya doke abokin hamayyarsa na Jam'iyyar PDP, Maj-Gen. Aminu Bande (mai ritaya).
Read More
Bilbis ya zama Sanatan Zamfara ta Tsakiya

Bilbis ya zama Sanatan Zamfara ta Tsakiya

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta bayyana ɗan takarar Sanatan Zamfara ta Tsakiya ƙarƙashin Jam'iyyar PDP, Ikra Aliyu Bilbis, a matsayin wanda ya lashe zaɓen sanata a yankin a zaɓen cike giɓin da da ya gudana Asabar da ta gabata. INEC ta ce Bilbis ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu mafiyawan ƙuri'u 102, 866 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin hamayyarsa na Jam'iyyar APC, Sanata Kabiru Garba Marafa, wandavya tsira da ƙuri'u 91, 216. Farfesa Kabiru Abdullahi na Jami'ar Tarayya da ke Gusau, shi ne ya kasance Baturen zaɓen da ya bayyana sakamakon zaɓen.
Read More
Sakkwato ta Arewa: Sanata Wamakko ya yi ta-zarce

Sakkwato ta Arewa: Sanata Wamakko ya yi ta-zarce

Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko na Jam'iyyar APC ya sake lashe zaɓen sanatan Sakkwato ta Arewa. Wamakko ya samu nasarar ce a zaɓen cike giɓin da INEC ta gudanar a ranar Asabar inda ya samu ƙuri'u 141,468. Abokin hamayyarsa na Jam'iyyar PDP, Dan’iya Manir Muhammad ne ya zama na biyu da ƙuri'a 118,445. Farfesa Ibrahim Magawata shi ne Baturen Zaɓen da ya bayyana sakamakon zaɓen da aka gudanar a rumfunan zaɓe 185.
Read More
Tambuwal ya sha da ƙyar a takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Tambuwal ya sha da ƙyar a takarar Sanatan Sakkwato ta Kudu

Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi nasarar lashe kujerar Sanatan Sakkwato ta Kudu da ya nema. Baturen zaɓen yankin, Farfesa Abubakar Abdullahi Bagudo, shi ne ya sanar da nasarar Tambuwal inda ya ce ya samu ƙuri'u 100,860 wanda hakan ya ba shi damar doke abokin karawarsa na APC, Sanata Ibrahim Abdullahi Danbaba wanda ya tsira da ƙuri'u 97,884. Nasarar Tambuwal ɗin dai na zuwa ne bayan da zaɓen kujerar ya kasance wanda bai kammalu ba a zaɓen yayin zaɓen 'yan Majalisar Tarayya da aka gudanar ran 18 ga watan Maris ɗin da ya…
Read More