Siyasa

NNPP na ƙoƙarin sauke nauyin da al’ummar Kano suka ɗora mata – ’Yankaba

NNPP na ƙoƙarin sauke nauyin da al’ummar Kano suka ɗora mata – ’Yankaba

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana ɗaukar nauyin duba masu larurar idanu kyauta da ba su magani da shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa ya yi da aka gudanar a Asibitin Gwagwarwa da cewa koyi ne da yake da Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf na baza ayyuka a ko'ina. Alhaji Yahuza Adamu 'Yankaba shugaban jam'iyyar NNPP na ƙaramar hukumar Nasarawa ne ya bayyana hakan. Ya ƙara da cewa shi kuma shugaban ƙaramar hukumar Nasarawa Ogan ɓoye ya yi amfani da wannan dama ya na ɗaukar marasa  lafiya da basu tallafi kamar yanzu yadda ya ɗauki masu larurar ciwon ido…
Read More
2027: Ganawar Kwankwaso da Obasanjo ba ta ɗaɗa Tinubu da ƙasa ba – APC

2027: Ganawar Kwankwaso da Obasanjo ba ta ɗaɗa Tinubu da ƙasa ba – APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC mai mulki ta ce ba ta jin tsoron ziyarar da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso, da tsohon gwamnan Jihar Kuros Riba, Donald Duke, suka kai gidan tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, da ke Abeokuta, Jihar Ogun, domin tattauna makomar siyasar Nijeriya. A cikin makonnin da suka gabata, an samu muhawara da ake yi kan zaɓen shekarar 2027, bayan da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Sanata George Akume, ya yi kira da a sake zaɓar Shugaba Bola Tinubu karo na biyu. A cewar Akume, ba za a samu gurbi…
Read More
Ba ma zawarcin Jonathan a takarar 2027 – PDP

Ba ma zawarcin Jonathan a takarar 2027 – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar jam'iyyar hamayya a Nijeriya, PDP, ta ce babu ƙanshin gaskiya a rahotannin da ake yaɗawa cewa ta nemi tsohon shugaban ƙasar, Dokta Goodluck Ebele Jonathan da ya tsaya mata takarar kujerar shugabancin ƙasar a shekara ta 2027. Jam'iyyar ta ce tana ta ganin ana yaɗa wannan batu, sai dai labarin babu gaskiya a ciki. Mai magana da yawun jam'iyyar na kasa, Ibrahim Abdullahi, shi ne ya musanta wannan labari a tattaunawarsa da BBC. Kakakin ya ce: ''To abin da ke gaskiya shi ne ba rahoton gaskiya ba ne na cewa jam'iyyar PDP ta…
Read More
Za mu gudanar da ayyukan cigaban al’ummar ƙaramar Hukumar Doguwa – Abdulrashid Rilwan

Za mu gudanar da ayyukan cigaban al’ummar ƙaramar Hukumar Doguwa – Abdulrashid Rilwan

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Zaɓaɓɓen Shugaban ƙaramar Hukumar Doguwa a Jihar Kano, Hon. Abdulrashid Rilwan ya bayyana cewa  abinda suka sa a gaba  a  yanzu a shugabancin ƙaramar hukumar shine su tabbatar da haƙƙin  al'ummar Doguwar yana zuwa  gare su ana yi musu ayyukan bunƙasa cigabansu. Ya bayyana haka ne da yake zantawa da manema labarai a Kano ya yi nuni da cewa akwai  ƙalubale da yawa da suke fuskanta a Doguwa  na  rashin ayyukan  cigaba  da ake fama dasu  a yankin sakamakon ana  turo tarin  haƙƙoƙinsu na  ƙaramar hukumar amma saboda azzalumai da Allah ya  ya haɗa su…
Read More
Dubban ‘yan PDP, APGA, YPP sun sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Zamfara

Dubban ‘yan PDP, APGA, YPP sun sauya sheƙa zuwa APC a Jihar Zamfara

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Ya'yan Jam’iyyar PDP su 1,500 da APGA da YPP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC a jihar Zamfara. Wannan na ƙunshe cikin wata sanarwa da Jamilu Iliyasu, mai taimaka wa shugaban kwamitin asusun kula da yanayin ƙasa kuma mai wakiltar Birnin Magaji/Kaura Namoda a majalisar wakilai, Jaji, ya fitar a ranar Litinin na Gusau. Ya ce waɗanda suka sauya sheƙar sun haɗa da shugabanni da magoya bayan jam’iyyar PDP da APGA da YPP da wasu jam’iyyu a jihar. Shugaban ƙungiyar jam’iyyar APC a jihar, Alhaji Isiyaka Ajiya-Anka, wanda ya wakilci ɗan majalisar, ya yaba…
Read More
Yadda korar tsohon kwamishinan El-Rufai a gwamnatin Kaduna ya ƙara rura wutar cece-kuce

Yadda korar tsohon kwamishinan El-Rufai a gwamnatin Kaduna ya ƙara rura wutar cece-kuce

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Korar Samuel Aruwan, tsohon kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna daga majalisar ministocin Gwamna Uba Sani ya ƙara ta’azzara cece-ku-ce game da tsamin dangantaka tsakanin gwamnan mai ci da kuma wanda ya sauka, Nasir El-Rufai. Fitar Aruwan dai ba ta kasance ba kwata-kwata, domin rahotanni sun nuna cewa ana takun saƙa tsakanin mambobin gwamnatin da ke da alaƙa da tsohon gwamnan. Aruwan, wanda tsohon ɗan jarida ne, ya taɓa zama mai bai wa El-Rufai shawara kan harkokin yaɗa labarai da wayar da kan jama’a daga shekarar 2015 zuwa 2019. Bayan zaɓen…
Read More
APC ta ƙaddamar da kwamitin sulhu a Jihar Adamawa

APC ta ƙaddamar da kwamitin sulhu a Jihar Adamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam’iyyar APC ta ƙaddamar da kwamitin sulhu mai mutum takwas domin gyara tsarin jam’iyyar da warware rikice-rikice a jihar Adamawa.  An bayyana wannan mataki ne a ranar Laraba a Yola, yayin wani taro da mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso Gabas, Mustapha Salihu ya jagoranta.  Sakataren yaɗa labarai na APC a Adamawa, Mohammed Abdullahi ya ce kwamitin na karkashin jagorancin Sanata Muhammed Mana.  Sanarwar da Manhaja ta samu ta bayyana cewa kwamitin ya ƙunshi wasu jiga-jigai kamar Sanatoci Bello Tukur, Abubakar Girei, Binta Garba da Injiniya Martins Babale.  Sauran 'yan kwamitin sun haɗa…
Read More
‘Yan majalisar Tarayya biyar sun sauya sheƙa zuwa APC

‘Yan majalisar Tarayya biyar sun sauya sheƙa zuwa APC

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan Majalisar Wakilai guda biyar daga manyan jam’iyyun adawa na PDP da LP sun sauya sheƙa zuwa APC. A zaman majalisar na ranar Alhamis shugaban majalisar, Abbas Tajuddeen ya sanar cewa ’yan jam’iyyar LP huɗu da wata ’yar PDP sun sauya sheƙa zuwa APC. Daga cikinsu har da ƙananan, ’yar gidan tsohon Gwamnan Jihar Delta, James Ibori. Mambobin LP da suka koma APC su ne, Donatus Matthew (Kaduna) da Tochukwu Chinedu Okere (Imo) da Akiba Bassey (Cross Riɓer) da kuma Esosa Iyawe (Edo). Masu sauya sheƙar sun danganta sauya sheƙar tasu da rikicin cikin…
Read More
APC na ƙara samun tagomashi ƙarƙashin jagorancin Ganduje – Kamalu Baƙo Lamiɗo

APC na ƙara samun tagomashi ƙarƙashin jagorancin Ganduje – Kamalu Baƙo Lamiɗo

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana fitaccen ɗan siyasa kuma ɗaya daga cikin dattawa a Jam'iyyar APC a jihar Kano,  Alhaji Nasiru Aliko ƙoƙi da cewa mutum ne mai son zaman lafiya da yake da kyakkyawar mu'amala tsakaninsa da  al'umma, ba kawai  'yan siyasa ba, da ma kowane irin mutum, shi ya sa duk wata hidima da ta taso masa ɗimbin mutane ke halarta. Hon. Kamalu Bawo Lamiɗo ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida a yayin ɗaurin auren ɗaya daga dattawan jam'yarr APC, Alhaji Nasiru Aliko da aka yi a unguwar ƙoƙi wanda ya samu…
Read More
Lauyoyi da dama ba su san me sabon ƙudurin haraji ya ƙunsa ba – Barau Jibrin

Lauyoyi da dama ba su san me sabon ƙudurin haraji ya ƙunsa ba – Barau Jibrin

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya bayyana cewa mafi yawan lauyoyi, har da wasu ‘yan majalisa, ba su fahimci abubuwan da dokokin gyaran haraji suka ƙunsa ba. A cewarsa, an hanzarta muhawarar dokokin zuwa karatu na biyu ne domin a bai wa al’umma damar tattaunawa da bayar da sharhi akansu. Dokokin gyaran harajin da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar wa Majalisar Dokoki a farkon watan Satumba sun haifar da cece-kuce, musamman daga yankin Arewa, inda ake ganin dokokin na iya ƙara tsananta matsin tattalin arziki a yankin. Gwamnonin Arewa, sarakunan gargajiya da wasu ƙungiyoyi sun yi watsi da…
Read More