Siyasa

APC ta nesanta kanta da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya

APC ta nesanta kanta da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Jam'iyyar APC na Ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya nesanta jam'iyyar da batun manyan muƙaman da aka naɗa a Majalisar Tarayya kamar yadda shugabancin majalisar dattawa da ta wakilai suka sanar a ranar Talata. Yayin taro da Kwamitin Gudanawar na Ƙasa na jam'iyyar da ƙungiyar gwamnonin APC a Abuja, Adamu ya ce Majalisar Tarayya ta saɓa ƙa'ida wajen sanar da manyan jami'an da aka naɗa ba tare da sanin jam'iyyar ba kamar yadda tashar AIT ta rawaito. A zaman da majalisun suka yi a ranar Talata aka jiyo Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar…
Read More
An yi naɗe-naɗen manyan muƙamai a Majalisar Tarayya

An yi naɗe-naɗen manyan muƙamai a Majalisar Tarayya

Daga BASHIR ISAH Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio da Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, sun yi naɗe-naɗe na manyan muƙamai a majalisar tarayya. A yayin zaman majalisun a ranar Talata Akpabio da Abbas suka sanar da naɗe-naɗen sabbin manyan muƙaman da aka yi. A Majalisar Dattawa, Akpabio ya ambaci Opeyemi Bamidele a matsayin Shugaban Masu Rinjaye, David Umahi a matsayin Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye; Mohammed Ali Ndume a matsayin Mai Tsawatarwa na Masu Rinjaye, sai Lola Ashiru a matsayin Mataimakin Mai Tsawatarwa na Masu rinjaye. Yayin da a Majalisar Wakilai kuwa, Abbas ya ambaci Julius Ihonvbere daga Edo a…
Read More
Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Rahoton EU: Atiku da Obi sun yi ca a kan Tinubu

Daga BASHIR ISAH 'Yan takarar shugaban ƙasa, Atiku Abubakar na Jam'iyyar PDP da Peter Obi na Jam'iyyar Labour a zaɓen 2023 da ya gabata, sun yi ca a kan Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, na ƙin yarda da rahoton ƙarshe da Ƙungiyar Tarayyar Turai (EU) ta fitar kan zaɓen shugaban ƙasa da ya gudana a ranar 25 ga Fabrairun da ya gabata. A ranar Talata, 27 ga Yuni, EU ta miƙa rahoton nata game da zaɓen a Abuja. Babban jami'in sanya ido, Barry Andrews, ya ce rahoton ya samo asali ne daga nazarin bin ƙa’idojin da Nijeriya ta ɗauka na…
Read More
Rigimar Majalisar Dokokin Nasarawa: Mambobin ɓangaren Ogazi na canja sheƙa zuwa ɓangaren Balarabe

Rigimar Majalisar Dokokin Nasarawa: Mambobin ɓangaren Ogazi na canja sheƙa zuwa ɓangaren Balarabe

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Idan ba a manta ba a 'yan kwanakin nan ne Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa ta tsunduma cikin rikici da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa jim kaɗan bayan zaɓen kujeral Kakakin Majalisar wanda aka so a gudanar a lokacin amma bai yu ba, inda a ƙarshe aka samu ɓangarori 2 tsakanin mambobin majalisar inda wasu ke goyon bayan tsohon kakakin majalisar, Ibrahim Balarabe Abdullahi wanda ke neman zarcewa a kujerar, yayin da wasu kuma ke tare da Ogah Ogazi da shi ma yake neman hawa kujera. Kodayake a lokacin ma fi yawan 'yan majalisar…
Read More
Shari’ar nasarar Tinubu: Lauyoyin Tinubu sun zargi Manhajar Amazon da haifar da matsalar da INEC ta samu da Rumbun IReV

Shari’ar nasarar Tinubu: Lauyoyin Tinubu sun zargi Manhajar Amazon da haifar da matsalar da INEC ta samu da Rumbun IReV

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaba Bola Tinubu ta bakin lauyoyinsa, ya shaida wa Kotun Sauraren Ƙararrakin Zaɓen Shugaban Ƙasa cewa Rumbun Adana Bayanai a Yanar Gizo na Amazon, ba shi da garanti, ya na iya samun matsala. Sai dai kuma wani ƙwararren injinijya na Amazon ya ƙaryata lauyoyin Tinubu ɗin. AWS Incorporated a ƙarƙashin Amazon ne suka buɗe wa INEC Rumbun Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe ta IReV, a lokacin zaven 2023. Atiku da Peter Obi duk sun ƙalubalaci ƙin watsa sakamakon zaɓe, wanda su ka ce ba a watsa a IReV ba, kamar yadda INEC ta yi alƙawarin…
Read More
A mayar da tsohon mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi da aka tsige kujerarsa – Kotu

A mayar da tsohon mataimakin gwamnan Zamfara Mahdi da aka tsige kujerarsa – Kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta bada umarnin mayar da tsohon Mataimakin Gwamnan Jihar Zamfara wanda aka tsige, wato Mahadi Aliyu Gusau kan kujerarsa. Mahadi dai shi ne Mataimakin Gwamna zamanin mulkin tsohon Gwamna Bello Matawalle, wanda aka tsige saboda ya ƙi bin shi Jam’iyyar APC daga PDP. Mahadi da PDP ne suka shigar da ƙarar suna ƙalubalantar tsige shi da Majalisar Dokokin Jihar ta yi a watan Fabrairun 2022. Da yake yanke hukunci a ranar Laraba, Alƙalin kotun, Mai Shari’a Inyang ya ce matakin da tsohon Gwamna Matawalle da kwamitin…
Read More
Gwamna Bala ya zama shugaban gwamnonin PDP

Gwamna Bala ya zama shugaban gwamnonin PDP

Daga BASHIR ISAH An zaɓi Gwamna Bala Mohammed na Jihar Bauchi a matsayin Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin PDP, yayin da Gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara, ya zama mataimakin shugaban ƙungiyar. An zaɓi Mohammed da Fubara ne a wajen taron bitar da PDP ta shirya wa zaɓaɓɓun jami'anta wanda ya gudana a Fadar Gwamnatin Jihar Bauchi a ranar Asabar. Gwamna Mohammed ya maye gurbin gwamnan Oyo ne, wato Seyi Makinde, wanda shi ma ya halarci taron na yini guda. Da yake jawabi a wajen taron, Shugaban riƙo na ƙasa na Jam'iyyar PDP, Umar Damagum, ya nuna wa jagororin buƙatar da ke akwai a…
Read More
Jam’iyyar Labour da Peter Obi sun kasa ci gaba da gabatar da bayanai a kotu

Jam’iyyar Labour da Peter Obi sun kasa ci gaba da gabatar da bayanai a kotu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Jam'iyyar hamayya ta Labour da ɗan takararta Peter Obi sun kasa ci gaba da bayar da bahasi a ƙarar da suka shigar a gaban kotun zaɓen shugaban ƙasa, a ranar Laraba. Kotun ta ba su ƙarfe 9 na safe a ranar Laraba, domin ci gaba da gabatar da bayanansu a gabanta ta hanyar kawo ƙarin shedu da takardu, inda aka ba su sa'a huɗu su yi hakan. Sai dai yayin da kotun ta zauna, lauyan masu ƙarar, Awa Kalu (SAN) ya gaya wa alƙali cewa sun shirya gabatar da wasu takardu, amma kuma suka…
Read More
Abin da Kwankwaso da Tinubu suka tattauna a ƙasar waje

Abin da Kwankwaso da Tinubu suka tattauna a ƙasar waje

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Ƙasa mai jiran gado, Bola Tinubu ya yi wata ganawar sirri da ɗan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Kwankwaso a ƙasar Faransa. Wata majiya mai tushe ta ce Tinubu ya yi wa Kwankwaso tayin tafiya tare da shi a sabuwar gwamnati da kuma duba yiwuwar sulhu tsakaninsa da Gwamnan Kano mai barin gado, Abdullahi Ganduje. A ranar Litinin, mako biyu kafin Tinubu ya karɓi rantsuwar fara aiki, suka shafe sama da awa huɗu suna ganawar sirrin da Kwankwaso a birnin Paris na ƙasar Faransa. Majiyarmu ta ce a yayin ganawar,…
Read More
Muna da kyakkyawar fata Atiku Abubakar zai nasarar zama Shugaban Ƙasa a kotu – Mai-Nasiha

Muna da kyakkyawar fata Atiku Abubakar zai nasarar zama Shugaban Ƙasa a kotu – Mai-Nasiha

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Wani ɗan Jam'iyyar PDP a Jihar Kano, Alhaji Salman Mai Nasiha ya bayyana cewa a yadda suke ganin ana gudanar da shari'ar ƙorafin zaven Shugaban Ƙasa a Babbar Kotun Abuja, suna kyautata zaton Atiku Abubakar zai yi nasara. Mai-Nasiha ya bayyana hakan ne yayin da yake hira da 'yan jarida, inda kuma ya yi nuni da cewa al'ummar ƙasar nan sun yi wa Buhari kyakkyawan zato a mulkinsa za su samu saulin rayuwa da walwala amma sai ga shi ya jefa mutane a mafi ƙuncin rayuwa da ba a tava tsammani ba. Ya ƙara da…
Read More