09
Feb
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rashin jituwa da ake zargi tsakanin tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i da gwamna mai ci a Kaduna, Sanata Uba Sani ya fito fili, bayan tsohon gwamna ya yi kakausan martani kan kalaman gwamna mai ci. Wannan sabuwar taƙaddama da ta kunno kai na da nasaba da kalaman da gwamna Uba Sani ya furta a lokacin wata hira da kafar talabijin ta TɓC a Nijeriya, wadda ba ta yi wa tsohon gwamna El-Rufa'i daɗi ba. Mutanen biyu waɗanda a baya aminan juna ne a fagen siyasa, abubuwa sun sauya tun bayan sauyin gwamnati da…
