06
Apr
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Ƙungiyar jajirtattun matasan jam'iyyar APC ta ƙasa, National Youths ɓanguard of APC ta sa ƙafa ta shure ɗaukacin zarge-zargen da Hon. Aminu Sani Jaji ya yi wa Ministan ƙasa a ma'aikatar tsaron Nijeriya, Dr Bello Muhammed Matawalle, cewa yana kitsa zarge-zargen ayyukan cin amanar jam’iyya a kansa. A cikin wata sanarwa da ta fitar, Sakataren yaɗa labaran ƙungiyar na ƙasa Dr Adeniyi Wale, ya bayyana zarge-zargen Hon. Jaji a matsayin “maras tushe,” yana mai cewa hakan wata hanya ce ta karkatar da hankalin jama’a daga abubuwan da yake kullawa a siyasa. “Jaji ya jima yana…
