25
Nov
Daga BASHIR ISAH Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, ta bada umarnin kan a sake gudanar da zaɓen Ningi ta Tsakiya a Ƙaramar Hukumar Ningi, Jihar Bauchi. Kakakin Majalisar Jihar Bauchi, Abubakar Suleiman, shi ne mai wakiltar Ningi ta Tsakiya a majalisar. A zaman da ta yi a ranar Juma'a, Kotun ta bada umarnin a sake zaɓe a rumfunar zaɓe guda 10 a yankin. Baturen zaɓe daga INEC, Farfesa Shuaibu Muhammad ne ya bayyana Suleiman a matsayin wanda ya lashe zaɓen da ya gudana a ranar 18 ga watan Maris, 2023. Suleiman wanda ɗan Jam'iyyar PDP ne, ya lashe zaɓe a…
