22
Feb
Ademola Lookman ya ce, ya ji takaicin irin kalaman da kocinsa Gian Piero Gasperini ya yi a kansa, bayan da ya kwatanta ɗan wasan da "wanda ya fi kowa rashin iya buga fenareti" da ya taɓa gani. Kocin ya yi kalaman ne bayan da Atalanta ta yi rashin nasara a hannun Club Brugge da ci 3-1 ranar Talata a gasar Zakarun Turai, abu kuma da ya sa ƙungiyar ta fice daga gasar da ƙwallo 5-1 gida da waje. "Abin ɓacin rai ne in yi martani a irin wannan rana, saboda abin da muka cimma a matsayin ƙungiya," kamar yadda Lookman…
