22
Mar
An kori ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Ibadan daga, Shooting Stars daga gasar Kofin Nijeriya ta shekarar 2025 bayan da aka same ta da laifin shigar da ‘yan wasan da ba su cancanta ba a wasansu na farko da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zamfara United FC. Oluyole Warriors, waɗanda tun farko suka tsallake zuwa zagaye na 32 sakamakon rashin halartar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Zamfara United FC, yanzu an kore su daga gasar. Wata wasiƙa daga hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) mai ɗauke da sa hannun daraktan gasar Ruth David, ta bayyana cewa Shooting Stars ta saka ‘yan wasa biyar…
