06
Feb
Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya yi barkwanci yana mai cewa yana ɗan jin haushin ƙungiyarsa, saboda abokan hamayyarsu sun fi su kashe maƙudan kuɗi wajen cefane. Man City ce ta fi kashe kuɗi a kasuwar saye da sayar da ’yan ƙwallo da ta ci ta watse a watan Janairu, inda ta sayi Antoine Semenyo daga Bournemouth da Marc Guehi daga Crystal Palace kan kusan fam miliyan 84 gabaki ɗayansu. Sai dai Guardiola ya ce abokan hamayyarsa a gasar Premier League sun fi zuba jari mafi yawa. Idan har za a yi ƙididdigar cefane, Man City ta kashe sama da…
