15
Nov
Kocin Manchester City, Pep Guardiala ya ja ragamar wasanni a 1,000 a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester City. Ya cika na 1,000 ne a Man City ta doke Liverpool 3-0 a wasan mako na 11 a gasar Premier League da suka fafata a Etihad ranar Lahadin da ta gabata. Man City ta fara cin ƙwallo ta hannun Erling Haaland a minti na 29 daga baya Nico Gonzalez ya ci na biyu, sai kuma Jeremy Doku ya kara na uku. Karo na 14 da Haaland ya zura ƙwallo a raga daga karawa 11 a Premier League a kakar nan - karo…
