04
Oct
Kocin Nottingham Forest, Ange Postecoglou ya buƙaci magoya baya su kara haƙuri, bayan da har yanzu bai ci wasa ba. Ranar Alhamis Forest za ta karɓi baƙuncin Midtjylland a Europa League a City Ground a karon farko tun bayan kusan shekara 30 rabon da ta shiga gasar zakarun Turai. Tsohon kocin Celtic da Tottenham ya maye gurbin Nuno Espirito Santo a watan Satumba, amma har yanzu bai ci wasa ba. Ya fara da shan kashi 3-0 a gidan Arsenal, sannan Swansea ta yi waje da su daga Carabao Cup da yin canjaras a Burnley da kuma a Real Betis a…
