20
Feb
Daga CRI HAUSA A wajen cikakken zama na 139 da kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na ƙasa da ƙasa wato IOC ya shirya a jiya Asabar a Beijing, shugaban kwamitin Thomas Bach, ya karrama al’ummar ƙasar Sin da kofin Olympics, da nufin gode musu saboda goyon-bayansu ga gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na bana. Bach ya ce, ba don goyon-bayan mutanen Sin ba, da ba za a iya shirya gasar bana tare da samun cikakkiyar nasara ba. Duk da cewa an shirya gasar bana cikin wani yanayi na kulle don hana yaɗuwar cutar COVID-19, amma Bach ya ji dadin…
