04
Mar
Daga CRI HAUSA A daren yau ne, za a buɗe gasar wasannin Olympics ta nakasassu ta lokacin hunturu ta Beijing a hukumance, inda yan wasan motsa jiki daga ƙasashen duniya za su yi ƙoƙarin samun nasara a wannan dandali mai muhimmanci. Shugaban kwamitin wasannin Olympics na nakasassu na ƙasa da ƙasa Andrew Parsons ya ce, masu aikin sa kai na birnin Beijing suna da himma da kwazo, yadda suke gudanar da ayyukansu, ya nuna min yadda alummar Sin suke karɓar baƙi da hannu bibbiyu. Ƙasar Sin ta duƙufa wajen shirya gasar wasannin Olympics ta nakasassu bisa Ƙa'idojin kare muhalli, yin…
