06
May
Kocin Real Madrid Carlo Ancelotti ya bayyana cewa, wataƙila ya yi ritaya idan ya bar ƙungiyar da ta zama zakarar gasar La Liga a bana, sai dai ya ce, a shirye ya ke ya cigaba da zama tare da qungiyar Madrid ɗin tsawon shekaru masu yawa a nan gaba. Ancelotti ɗan ƙasar Italiya mai shekaru 62 a duniya, ya zama koci na farko a tarihi da ya lashe kofunan manyan lig-lig guda biyar na Turai, nasarar da ya cimma a wannan kakar tare da Real Madrid bayan lashe gasar La Liga, inda kuma ya jagoranci karawa da Manchester City ranar…
