Me shugaban IOC ya shaida wa jagoran CMG?

Daga CRI HAUSA

A jiya Talata ne shugaban kwamitin shirya gasar Olympic ta ƙasa da ƙasa IOC Thomas Bach, ya miƙa wa shugaban babbar kafar watsa shirye-shirye ta ƙasar Sin CMG Shen Haixiong, kofin karramawa a nan birnin Beijing, bisa gudummawar da shi kan sa, da ma CMGn suka bayar, wajen watsa wasannin wannan muhimmiyar gasa.

Yayin da yake karɓar wannan kyauta, Shen Haixiong ya ce wannan nasara ce ta ɗaukacin masu ruwa da tsaki, kuma wannan karramawar ta IOC, ta tabbatar da ƙwazon CMG, da ma ɗaukacin kafofin watsa shirye-shirye na Sin, bisa ƙoƙarin su na yayata ruhin Olympic, da watsa shirye-shiryen gasar ta birnin Beijing.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *