Wasanni

Juan Antonio Samaranch Jr.: Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta zarce tunanin IOC

Juan Antonio Samaranch Jr.: Gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta zarce tunanin IOC

Daga CRI HAUSA Bisa la’akari da yaɗuwar annobar COVID-19, ayyukan shirya gasar Olympics ta lokacin huturu ta Beijing, sun kasance masu matuƙar wahala, sai dai sun samu kyakkyawan yabo. Shugaban kwamitin taimakawa shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing ta shekarar 2022 na kwamitin wasannin Olympic na duniya IOC, wato Juan Antonio Samaranch Jr. ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, duk da muhawarar da ake tafkawa kan ƙasashe masu karɓar baƙuncin gasanni da kwamitocin shirya gasannin, kwamitin IOC bai taɓa shakkun ƙarfin ƙasar Sin na karɓar baƙuncin gasar ba, haka kuma ayyukan shirya gasar da…
Read More
Sannu a hankali wasannin ƙanƙara na samun karɓuwa a ƙasar Sin

Sannu a hankali wasannin ƙanƙara na samun karɓuwa a ƙasar Sin

Daga CRI HAUSA Tun bayan ƙasar Sin ta fara shirya gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta shekarar 2022, an gudanar da wasannin ƙanƙara iri daban-daban na jama’a, a wurare daban-daban na ƙasar. Kana an gina wuraren wasannin ƙanƙara masu kyau, waɗanda suka sa ƙaimi ga ƙarin mutane zaɓar shiga wasannin ƙanƙara. Yanzu, Sinawa na iya wasannin motsa jiki a duk shekara, ko lokacin zafi ko kuma lokacin sanyi. Wasannin motsa wata hanya ce ta kyautata zaman rayuwar jama’a. Bisa ƙididdigar da aka yi, yawan mutanen da su kan motsa jiki a birnin Beijing ya kai kashi 50.18 na adadin…
Read More
Nijeriya da Ghana za su fafata kan tikitin zuwa Kofin Duniya

Nijeriya da Ghana za su fafata kan tikitin zuwa Kofin Duniya

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Nijeriya (NFF) ta bayyana cewa, tawagar ’yan wasan ƙasarta na Super Eagles za su fafata da takwarorinsu na Ƙasar Ghana a wasan neman tikitin zuwa Gasar Cin Kofin Duniya da Ƙasar Ƙatar za ta karɓi baƙunci a filin wasa na MKO Abiola da ke birnin Abuja. Sanarwar ta NFF ta ce, za a yi wannan karawar ne a ranar 27 ga watan Maris.A halin yanzu a na dakon sanarwa daga Hukumar Ƙwallon Ƙafar Ghana kan zagayen farko na wasan neman cancantar da za su buga, wanda ake sa ran ya gudana ko dai a ranar 23 ga…
Read More
CMG ya samar da kyamara mai saurin ɗaukar hotunan bidiyo domin gasar wasannin Olympics ta Beijing

CMG ya samar da kyamara mai saurin ɗaukar hotunan bidiyo domin gasar wasannin Olympics ta Beijing

Daga CRI HAUSA Babban gidan rediyo da talibijin na ƙasar Sin na CMG ya ƙera wata kyamara mai ƙarkon gaske, bisa fasahar “Ultra HD 4K” domin amfani da ita wajen ɗaukar hotunan bidiyo masu nagarta. Kyamarar dai na iya zarta gudun ‘yan wasan dake tsere a dandamalin ƙanƙara, yayin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing dake gudana yanzu haka. An kafa kyamarar a cikin zauren tseren ƙanƙara na babban filin wasan hunturu dake birnin Beijing, inda kyamarar da aka yi wa laƙabi da "Cheetah," kan yi gudun mitoci 25 ko wace daƙiƙa, wato kwatankwacin gudun kilomita 90 ko…
Read More
Sayayya 10 mafi tsada a tarihin ƙwallon ƙafa

Sayayya 10 mafi tsada a tarihin ƙwallon ƙafa

A halin yanzu, yayin da duniya ke jiran a tabbatar da cinikin Paul Pogba wanda zai kama kusan fam miliyan £100 daga Juventus zuwa Man Utd, idan hakan ta tabbata, to zai zama sayayyan da ya fi kowane tsada a duniya. Blueprint Manhaja ta kawo maku sauran sayayyen da su ka fi kowane tsada a duniya. Ban da shahararru irin su Cristiano Ronaldo da Bale da aka sani, akwai wasu hala waɗanda ba a sani ba. Ga dai jerin ’yan wasa 10 nan, waɗanda cinikin su ya fi na kowa tsada a duniya. Ƙungiyar Man City, wanda ta yi ƙaurin…
Read More
Aubameyang ya buƙaci ninkin albashin Ibrahimovic a AC Milan

Aubameyang ya buƙaci ninkin albashin Ibrahimovic a AC Milan

Ɗan wasan gaba na Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang, yana neman sau biyu abin da Zlatan Ibrahimovic yake samu a AC Milan don komawa qungiyar ta qasar Italiya. AC Milan ita ce kulob na baya-bayan nan da ake alaƙanta ta da ɗan wasan mai shekaru 32, wanda a yanzu ba a san makomar shi ba a Emirates. Tun a ranar 6 ga watan Disamba, Aubameyang bai taka leda a Gunners ba, lokacin da Arsenal ta sha kashi da ci 2-1 a Goodison Park. An cire ɗan wasan na Gabon ne daga muƙamin kyaftin ɗin ƙungiyar bayan mako guda bayan wani sabon ladabtarwa…
Read More
Joshua ya musanta karɓar cin hanci don fasa karawa da Usyk

Joshua ya musanta karɓar cin hanci don fasa karawa da Usyk

Fitaccen ɗan damben ‘boxing’ ajin masu nauyi, Anthony Joshua ɗan Ingila, ya yi watsi da rahotannin cewa ya amince da yarjejeniyar karɓar kuɗi fam miliyan 15 kwatankwacin Yuro miliyan 18 don janyewa daga shirin sake karawa da Oleksandr Usyk na ƙasar Ukraine. A watan Satumban shekarar bara ne dai Usyk ya kwace dukkanin kambun Joshua na WBA da IBF da kuma WBO, bayan lallasa Joshua ɗin da yayi a fafatawar da suka yi. Rashin nasarar da Joshua ya yi a karon battarsa da Oleksandr Usyk, ita ce karo na biyu da fitaccen dan damben boxing ɗin ya fuskanta tun bayan…
Read More
Everton ta kori Rafael Benitez kwanaki 200 bayan ba shi aikin horarwa

Everton ta kori Rafael Benitez kwanaki 200 bayan ba shi aikin horarwa

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta kori Manajanta Rafael Benitez kwanaki 200 cif bayan ba shi aikin horarwa daidai lokacin da ƙungiyar ke ci gaba da fuskantar tarin rashin nasara a wasanninta na Firimiya. Benitez wanda ya yi aiki tsawon lokaci da Liverpool da ke matsayin babbar abokiyar dabin Everton ya karɓi ragamar ƙungiyar ne a watan Yunin 2021. Sanarwar da ƙungiyar ta wallafa a shafinta ta tabbatar da raba gari da kocin nata bayan shan kaye a wasanni 9 cikin wasanni 13 da ƙungiyar ta doka a baya-bayan nan ƙarƙashin gasar firimiyar Ingila. Rashin nasara ta baya-bayan nan da…
Read More
Shugaba Buhari ya aika da saƙo ga kocin Super Eagles

Shugaba Buhari ya aika da saƙo ga kocin Super Eagles

Daga WAKILINMU Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buƙaci kocin Super Eagles, Austin Eguavoen da ya ci gaba da kuma zarce yadda ya kai ga nasara a gasar cin kofin Afrika (AFCON) da ake yi a Kamaru. A cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Larabar da ta gabata ta hannun mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina, Buhari ya bayyana cewa ƙasar na fatan samun nasara guda bakwai a gasar. Shugaba Buhari ya yaba wa ƙungiyar bisa ƙoƙarinta na lashe dukkan wasanninta na rukuni wanda ya sa ta tsallake zuwa zagaye na biyu a…
Read More
Messi na iya girgiza magoya bayan Barcelona a dalilin iyalansa

Messi na iya girgiza magoya bayan Barcelona a dalilin iyalansa

Ɗan wasa Lionel Messi zai iya dawowa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona sakamakon iyalansa basajin daɗin zama a babban birnin France Paris. Iyalan ɗan wasan gaban ƙasar Argentina da Paris saint-german Lionel Messi sun bayyana masa ƙarara cewar ba su jin daɗin zama a babban birnin ƙasar Faransa wato Paris. Iyalan na Lionel Messi sun fi jin daɗin zama a birnin Barca da ke ƙasar Sifaniya kafin subar ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona. A bayyane yake cewar Lionel Messi zai iya komai domin iyalansa kuma wannan dama ce da Barcelona za ta yi yunƙurin dawo da shi filin wasa na…
Read More