Dalilin fuskantar ƙarancin bizar Umara a Ramadan – NAHCON

Daga BASHIR ISAH

Hukumar Aikin Hajji ta Ƙasa (NAHCON), ta bayyana cewa, rashin amfani da bizar da Saudiyya ta bai wa wasu ‘yan Nijeriya tun farko, shi ne ya haifar da cikas wajen samun sabuwar biza ga masu shirin tafiya Umara a wannan wata na Ramadan.

Rahotanni sun nuna yadda ‘yan Nijeriya ke fama ainun wajen neman bizar da za ta ba su damar tafiya Umara a Saudiyya a watan Azumin Ramdan.

Sanarwar da NAHCON ta faitar a ranar Talata ta bakin kakakinta, Fatima Sanda Usara, ta ce Saudiya kan ba da bizar Umara ga ƙasashe ne gwargwadon yawan mabuƙata, tare da cewa da ma ita bizar Umara a Ramadan ta fi ta sauran lokuta tsada.

Ta ƙara da cewa, yayin da Saudiyya ta ƙara wa’adin amfanin bizar zuwa kwana 90, sai dai galibin ‘yan Nijeriya sun mallaki tasu bizar ce a farashi mai sauƙi kuma a wasu lokuta na daban da nufin za su yi amfani da bizar don tafiya Umara a Ramadan.

“An fuskanci ƙaranci ƙaranci bada biza ga ‘yan Nijeriya ne sakamakon wasu sun tsawaita wa’adin zamansu a Saudiyya, ko kuma sun mallaki bizar tun a baya amma suka ƙi yin amfani da ita domin jiran Ramadan, wanna shi ya yi silar fuskantar ƙarancin gurbin samun sabuwar biza ga ‘yan ƙasar,” in ji sanarwar.

Fatima ta ƙara da cewa, ƙaruwar masu buƙatar biza yayin Ramadan, ita ma ta taimaka wajen fuskantar ƙarancin samun bizar.

Sai dai ta ce an duƙufa ganin yadda za a shawo kan wannan matsalar, tana mai cewa, ofishin NAHCON da ke Saudiyya ya ba da himma wajen tattaunawa da Ofishin Hajji da Umara na Saudiyya don cimma nasara.