Bahaushe na cewa ‘Damina Uwar Albarka!’ Wannan magana ta Malam Bahaushe haka ta ke, domin a lokacin damina ne ake samun albarkatu masu yawa, musamman a fannin abinci, a lokacin ne ake samun abincin da ake ci, wanda kuma abinci ne jigon rayuwar kowane halitta. Kuma alhamdu lillahi, ya zuwa yanzu za mu iya cewa damina ta kankama, sai dai fatan Allah ba mu dacewa.
Duk da cewa a wannan zamani na damina, lokaci ne da ake samun albarkatu masu yawa, to haka kuma akwai wasu bala’o’i da sukan samu ɗan adam, waɗanda a lokuta da dama ma har abin ya kan kai ga cin rayuka, baya ga asarar dukiya.
Damina ta kan kasance lokaci ne da ake samun raguwar munanan ayyuka, domin a lokacin ne ake samun matasa masu yawan gaske, waɗanda suka tare a bariki, amma duk sun koma ƙauyukansu sun duƙufa a harkar noma.
Wannan ne ma ya sa da zarar ruwan shuka ya sauka za a tarar da yawancin masu ayyukan ƙarfi sun ragu, sun koma garuruwansu, hatta ma su almajirai masu karatun allo sukan ragu a bariki a daidai wannan lokaci, domin sun tafi garuruwansu domin yi wa Malamansu noma, wasu kuma sukan tafi garuruwansu wajen iyayensu don taya su noma.
Shi ya sa ma a daidai wannan lokaci gwamnatoci ke samar da takin noma, kuma sukan yawaita kira ga jama’a, musamman matasa su koma gona, domin shi aikin gona yana zama wata babbar hanya ta samar da aikin yi.
Baya ga waɗannan muhimman abubuwa masu amfani da Damina ke da su, akwai abubuwa, kamar yadda muka faɗa a sama, masu haxari, waɗanda ya wajaba a mayar da hankali wajen kiyaye su.
Don haka akwai matuƙar muhimmancin ɗaukan matakan da suka wajaba don kare lafiyar jiki da ta dukiya da ta muhalli, musamman, domin akwai matakan da suka kamata a ɗauka don kauce wa kamuwa da cututtukan da ambaliyar ruwa, wanda wannan yanayi na Damina kan haddasa.
Lokacin Damina, za mu iya cewa lokaci ne mai haɗari, musamman wajen kamuwa da cututtuka ko ambaliyar ruwa, domin a lokacin ne ake samun yaɗuwar cututtuka daban-daban, musamman a yankunanmu na karkara da kuma wuraren da ba su da yanayin samun magudanan ruwa.
A wannan lokaci na Damina, akwai abubuwa da dama da suka wajaba a kula da su, amma dai muhimman abubuwan da za a fi mayar da hanakli, su ne samar da magudanan ruwa, da kuma kariya daga cizon sauro. Waɗannan abubuwa ne da galiban ake samun matsala da su a lokutan Damina, waɗanda kuma su ne suka fi ba da wahala a rayuwar ɗan adam.
Domin rashin samar da magudanan ruwa suna haddasa mummunan ambaliyar ruwa, sannan akwai cututtuka masu haɗari da akan kamu da su a sanadiyyar haka, musamman varkewar annobar kwalara, da kuma wasu cututtukan da su ma sukan faru a sakamakon wannan yanayi.
A irin wannan lokacin ne masana yanayin muhalli kan ta wayar da kan jama’a game da muhimmancin kiyaye aa’idojin da aka shata wajen kula da muhalli, inda har ma a wasu lokuta sukan yi jan hankali da gargaɗin cewa za a iya samun ambaliyar ruwa a wasu jihohi.
Masanan harkar lafiyar kuma sukan yi bayanin cewa, a wannan lokaci ana yawan kamuwa da cututtukan da suka haɗa da zazzaɓin cizon sauro, cutar kwalara da dai sauransu da dama.
Wani Likita da ke aiki a wani babban asibiti ya bayyana cewa, a duk lokacin da aka shiga wannan yanayi, sukan samu qarin marasa lafiya nunkin-banunkin waɗanda su ke samu kafin shigar yanayin, musamman a ɓangaren da cututtukan ke haddasawa.
Ya ce, a wannan lokacin Likitoci sukan shiga wayar da kan jama’a gadan-gadan don ganin sun samu wayewa kan yanayin da suka samu kansu, da kuma matakan da za su bi wajen kare kansu daga cututtukan da suke shiga jikin ɗan adam da kuma yanayin da akan samu ambaliyar ruwa a daidai lokaci irin wannan.
Likitan ya kuma bayyana cewa, cututtuka na samun sakewa a lokacin Damina a jikin ɗan adam fiye da kowane lokaci, musamman zazzaɓin cizon sauro, da dai sauransu. Sannan kuma a wannan lokaci ne ake samun wani hatsabibin ƙuda da ke yaɗa cututtuka da addabar jama’a.
Wannan ne ya sa mu ke ganin ya kamata Hukumomi da sauran ƙungiyoyin bayar da agaji na ƙasa da ƙasa, da sauran ƙugiyoyi da hukumomin ƙasar nan da na duniya su shiga aiki wajen bayar da gaji, musamman na wayar da kan jama’a a wannan yanayi, musamman wajen binciken don gano wurare da aka iya samun ambaliya don su kiyaye.
Babban aiki ne da ke gaban Hukumomi, irinsu NEMA, SEMA, RED CROSS da sauran ma’aikatun kiwon lafiya da na jin ƙai na jihohi da na tarayya da ma sauran ƙugiyoyin kiwon lafiya masu zaman kansu, da masu kula da muhalli, su fito domin taimakawa wajen wayar da kai a wannan yanayi da muka shiga.
Duk da ya ke dai a bana ba a samu wata barazar ɓarkewar ambaliya ba, amma yana da muhimmanci kowa ya zama ya ɗauki matakan kare kai, musamman wajen tsaftace muhalli, abinci, wurin kwana, tare da kiyaye zama a kusa da rafuka ko manyan hanyoyin ruwa. Kamar dai yadda hukumomi ke ta jan hankali.
Domin su cututtuka irin waɗannan a kowane lokaci babu abin da ke yaɗa su cikin saurin kamar ƙazanta ko rashin tsafta ko kuma toshe magudanan ruwa, wannan kuma ita ce babban matsalar da ke damun al’ummarmu, musamman na yankunan karkara.
Haka kuma akwai jan aiki a gaban shugabannin addini wajen yin kira ga magoya bayansu wajen ɗaukar matakan da mu ka lissafa a sama, da ma wasu da ba mu ambata a nan ba. Wannan kuwa ya zama wajibi ne bisa la’akari da irin muhimmancin da shugabannin addini ne da shi a tsakanin jama’a.
Mu na addu’a, Allah ya kare mu daga kamuwa da duk wata cuta da za ta addabe mu, tare da neman kariya daga mummunar ambaliyar ruwan da za ta raba mu da muhallanmu. Amma dai yana da kyau a ɗauki matakan da suka dace.