Dandalin shawara: Mijina ba ya fashin kusanta ta lokacin da nake jinin al’ada

(Ci gaba daga makon jiya)

Daga AISHA ASAS

TAMBAYA:

Assamu alaikum wa rahmatullahi. Hajiya Aisha ya ƙoƙari. Ya kuma fama da jama’a. Kwana da yawa. Fatan duk iyalai lafiya. Sunana…………daga nan………….. Mun ɗan yi magana da ke a shekarun baya, lokacin littafinki na ‘Soyayyar Ƙarya’, har ki ka ba ni shawarwari kan matsalata, kuma na ji daɗin su ainun, don sun fitar da ni matsalar. To yanzu ma wani abu ne ke ci min turo a ƙwarya. Wallahi mijina ne dai al’amarinsa ya fara damuna, matsala ce da ta kai kusan shekara yanzu, muna iya kwashe kusan sati uku zuwa huɗu bai damu da neman haƙƙinsa na aure ba, amma da an ce ma ki na fara jinin al’ada to fa ba fashi, duk dare sai ya kusance ni, har tambaya yake yaushe ne zai zo. Mijina na da zafi, amma akan kusanta ta lokacin al’ada idan na hana shi zai ta rarashi na, sam ba ya fushi. Rabon da ya kusance ni Ina da tsarki har na manta. Da abin ya dame ni ne, na ce, bari na sake taɓo ki, don na san zan sami mafita. Me ya kamata na yi, Hajiya Aisha.

AMSA:

Idan za mu yi duba da dalilin haramtar wannan kusanta, za mu iya cewa, tana da cutarwa ga mai aikatawa, dalilin kuwa, a cikin wani littafi mai daɗaɗɗen asali, wanda wani shehin malami ya yi, da ke taimaka wa wurin amsa tambayoyin fiƙihu, ya ce, “mai shar’antawa (Allah kenan) ba ya umurni da yin abu face abun ya kasance alkhairi ne tsagaro(ga mai aikatawa), ko alkhairin ya rinjaye sharrin. Kuma ba ya hani kan wani abu, face abun ya kasance sharri ne tsagaro (ga mai aikatawa) ko sharrin ya rinjaye alkhairin.”

Da wannan zan ce mu yi duba ga mafi yawan ababen da Musulunci ya hane mu da waɗanda ya umurce mu da yi, misali, aure da zina. Ya ce mu yi aure, mu tsaya ga halastattun mata da mazanmu, ta bin wannan kawai za mu iya kuvutar da kanmu daga cutuka masu yawa. Ya ce kada mu yi zina, ta bijirewa wannan umurni mun sani akwai ababe da dama da za mu iya cin karo da su da za su cutar da jikinmu.

Misali na biyu saki da idda. Yin saki yana cikin ababen da ba a son yi, amma a wani ɓangare yana da amfani shi ya sa aka halasta shi, saboda ta sanadiyyar rashin saki za a iya haɗuwa da matsalar ƙwaƙwalwa ta hanyar zaman uƙuba, musamman ga mata, ko zaman tauye jiki ta sanadiyyar rashin ba shi haƙƙinshi, kai har zai iya kai ga kisa ma, ta sanadiyyar ganin ita ce hanyar da kawai zata iya kawo ƙarshen zaman rashin so da ake yi.

Idda kuwa, kamar yadda wani likita ya faɗa, ita ce hanya mafi inganci da ya tava gani da ke tsarkake mace daga wani namiji zuwa wani. Kamar yadda ya ce, ba kawai hanya ce ta tabbatar ba a kai cikin wani gidan wani ba, hanya ce da zai nisanta ka daga cutukan saduwa da dama, irin waɗanda ake ɗauka don saduwa kawai (kamar su gunoriya, STD waɗanda ba su shafi cutar jini ba ba kamar HIV da makamantan ta), a cewar sa, ya yin da mace ta yi jini ukun duk wannan matsalar tana wankewa albarkacin jinin haila.

Idan muka ɗauki matsalar da ki ke da ita ‘yar’wa, za mu tarar da matsala a tattare da ita da Musulunci ya riga mu hango ta. Ko Bature da ya zama allon kwaikwayon mu, ko ince bincike nasa da bai haramta saduwa a lokacin jinin ba, ya tabbatar da cewa, akwai yiwa mai ƙarfi ta saurin kamuwa da cutuka cikin sauqi a wannan yanayi wanda bai kai idan ana da tsarki ba. Shi ma kenan bare idan kin koma ga likitancin gaskiya, na Ma’aikin Allaha. A taƙaice ci gaba da biye wa mijinki tamkar kin yanke lasisin kamuwa da wasu cutuka ne, wanda kowacce mace da ire-iren waɗanda za ta iya kamuwa da su.

Jinin haila kamar yadda littafi mai tsarki ya ambata ƙazanta ce, domin hanya ce ta wanke datti da kwamacalar da mace ta tara tsayin wata, a wata fassara gidansu ɗaya da kashi da fitsari da muke fitarwa, kuma bola ce a fassarar marar hankali da ake buƙatar ta fita don tsaftace muhalli, kinga kuwa hatsari ne shiga cikin wannan kayan dauɗa, ga mai shiga da kuma wanda ya bari aka watse ma shi sharar, sai dai illar ta fi yawa ga macen ita da abin yake cikin jikinta, kuma ba wata hanyar kare dauɗar ga zuwa inda ba a so ta kai.

Shawara ki ji tsoron Allah, ki sani babu hanya mai vullar da ke duk cikin hasashen dalilan da suka sa mijinki wannan ɗab’a. Shawarar da za mu ba ki mataki-mataki ce, na farko ki sa wa ranki kin daina bari wannan abu ya faru, kuma ki riqe wuta, ki sha alwashin matuƙar da amincewar ki mijinki zai kisance ki lokacin al’ada ba za a sake ba.

Na biyu, ki ilimintar da shi illa da haramcin wannan abu idan kina da sani kan haka, idan ba ki da, sai ki nemi makusancin sa kuma mai amanar riƙe sirrin ki sanar da shi, amma zai fi kyau idan ke da kanki ki ka yi hakan, wannan zai yiwu ne idan har yana yi ne bisa ga jahilci.

Idan ƙiyawar da kuma nasiha ba su yi tasiri ba, sai mataki na gaba, shine shigowar manya, ki sanar da makusantan shi, waɗanda yake jin maganar su, amma zai fi ki fara da namiji ba mace ba, ma’ana babanshi ko cikin ‘yan’uwan iyayenshi da suka fi shaƙuwa, kuma ki yi hattara yayin zavar, domin akwai waɗanda zai fi son ya mutu da su san yana aikata aikin assha, kinga kuwa idan kin yi amfani da su wata matsalar za ta sake ɓullowa.

Irin waɗannan mutane ana amfani da su ne a mataki na ƙarshe, wato idan an bi duk wata hanya ya qi canzawa, to za ki yi amfani da irin waɗannan mutane idan yana da su, ko kuma ki sanar da danginki, hakan zai sa su shiga lamarin sosai, idan ba abu ne mai canzawa ba, to za su raba auren, wanda Musulunci ya aminta da haka, kuma ke hakan zai taimake ki a gaba, kuma kin tsiratar da lafiyarki kin kuma bi umurnin ubangiji, kinga kuwa ba za ki tave ba. Shi kuma ko ma meye dalilin shigar sa wannan ɗabi’a ba da ke za a ga sakamako ba, idan ma tsafi ne, kin kuvuta.

Allah Ya yi ma ki duk abinda yake alkhairi, Ya shirya mi ki mijinki, idan zaman naku tare ne alkhairi, idan da cutarwa, Allah Ya yi ma ki musanya da wanda ya fi shi.

Zavin Allah shi ne mafi daidai ga bayinSa, domin Shi ya san abinda yake bayyane da voye.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *