Yadda fitaccen biloniya ya yi asarar kaso 93% na dukiyarsa a Chana

Daga AMINA YUSUF ALI

Shahararren attajirin biloniyan nan ɗan ƙasar Chana mai suna, Hui Ka Yan ya yi asarar kaso 93% na dukiyarsa. 

Hui Ka Yan, shi ne shugaban rukunin kamfanoni na  kamfani na Evergrande Group a lasar Chana. Kafin dukiyar tasa ta dulmiye, ya kasance yana da ƙarfin arzikin da ya kai Dalar Amurka biliyan 42. Amma zancen da a ke yi yanzu, dukiyar tasa ta dulmiye i zuwa, Dalar Amurka biliyan uku kacal!

Biloniyan na ƙasar Chana, ya kasance ɗaya daga cikin hamshaƙan Attajirai masu dukiya da ƙasar ta Chana take ji da su. Amma a halin da ake ciki a yanzu, bai mallaki abinda ya wuce Dalar Amurka biliyan uku ba kamar yadda kafar labarai ta CBN ta rawaito. 

Evergrande shi ne ma fi girman kamfani mai cigaba da yake da zunzurutun kadara da ta kai ta Dalar Amurka biliyan $300. Kuma ya kasance gaba-gaba wajen warware matsalar hada-hadar  gidaje da filayen a ƙasar Chana a shekarar 2021. Don ceto kamfaninsa daga dulmiyewa, Attajirin ya sayar da gidaje da jiragen samansa na ƙashin kai. 

Kamfanin yana da ma’aikata 200,000, kuma a shekarar 2020 ya samu ribar kimanin Dalar Amurka biliyan $110 a cinikinsa. Sannan ya na da harkokin fiye da 1,300 a garuruwa 280. 

Sai dai ana zargin cewa, babban abinda ya jawo masa karayar arziki ba ya rasa nasaba da wariyar launin fata da yake fuskanta a siyasance. Majalisar da ta qunshi manyan mutane ta ƙasar Chana (CPPCC) ta ware shi daga majalisar tuntubar wacce ta haɗa dukkan masu ilimi da masu kuɗi da sauran masu faɗa a ji a qasar ta Chana wacce yake ciki tun shekarar 2008.  

Daga lokacin da kamfaninsa ya fara yin ƙasa a shekarar bara, majalisar ta hana shi halartar taronta na shekara-shekara. Sannan an cire sunansa daga jerin sunayen mutanen da za su haɗa CPPCC nan da shekaru biyar masu zuwa.