EFCC ta farauto fiye da Naira Biliyan 201 na kuɗaɗen harajin ma’adanai daga kamfanoni

Daga BAKURA MUHAMMAD a Bauchi

Hukumar Yaƙi da yi wa Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC), ta bayyana cewar ta farauto zunzurutun kuɗaɗe fiye da Naira biliyan 201 kuɗaɗen harajin ma’adanai daga kamfanonin man fetur da ya kamata su bai wa Hukumar Bunqasa Cigaban Yankin Neja Delta (NNDC) da suka yi wa Hukumar Daidata Ƙa’idojin Haƙo da Man Fetur (NUPRC) ƙurmusu.

Shugaban hukumar ta EFCC, Abdulrasheed Bawa shi ne ya yi wannan furuci yayin da yake yin jawabin manema labarai a wani shirin faɗakarwa da tawagar manema labarai a fadar shugaban ƙasa ta shirya makon jiya.

Ya ce daga cikin wannan adadi, an jaddada mallaka wa Hukumar Raya Cigaban Yankin Neja Delta (NNDC) Naira biliyan talatin.

Bawa ya bayyana cewar: “Ga wasu daga cikin abubuwa da muka gudanar dangane da zaƙulo kuɗaɗe a watan Nuwamba na wannan shekara, 2022. Mun samar da Dala miliyan 354 wa hukumar NUPRC kuɗaɗen harajin ma’adanai waɗanda ɗaya daga cikin kamfanonin man fetur bai biya ba. Binciken mu ne ya samar da waxannan kuxaxen.

“Dangane da zaƙulo kuɗaɗe na hukumar NNDC da muke yi kuwa, tsakanin makon da ya gabata da wanda yanzu muke ciki lokaci, za mu tura wa hukumar kuɗi kimanin Naira biliyan talatin da kuma kimanin Dalar Amurka miliyan talatin.”

Shugaban hukumar ta EFCC ya ce, “waɗannan kuɗaɗe ne da muka zaƙulo daga kamfanonin man fetur kashi uku cikin ɗari da ya wajabta su biya, amma suka yi ƙurmusu ko ƙememe da biyan kuɗaɗen wa hukumar NNDC.”

Bawa yaƙi shaida wa manema labarai adadin kamfanoni da suka yi ƙurmusun biyan kuɗaɗen harajin, yana mai cewar, “daga kamani ɗaya ne tal muka zaƙulo waɗannan kuɗaɗe Dala miliyan 354.