Gwamnan Zamfara ya yi wa fursunoni 46 afuwa

Daga MUHAMMAD SANUSI, a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara, Bello Mohammed Matawalle, ya yi wa fursunoni 46 a jihar.

Fursunonin da afuwar ta shafa waɗanda kotunan shari’a na jihar suka yanke musu hukunci ne tare da tsare su a gidan yari a Gusau.

Babban Lauyan jihar kuma Kwamishinan Shari’a, Barista Junaidu Aminu Kaura ne ya bayyana haka a lokacin da yake zantawa da manema labarai a hedikwatar gidan gyaran hali ta jihar da ke Gusau a ranar Juma’a.

A cewarsa, waɗanda aka yi wa afuwar sun haɗa da fursunoni 30 da aka yanke wa hukunci daban-daban na ɗaurin shekaru 20 zuwa daurin wata shida da mutum tara da aka yanke wa hukuncin rai-da-rai da kuma fursunoni 11 da aka yanke wa hukuncin kisa.

Kwamishinan ya bayyana cewa yafe wa fursunonin ya biyo bayan shawarar da kwamitin jin ƙai da ke ƙarƙashinsa ya bai wa ofishin Gwamna ne.

Ya ce, Gwamnan ya amince da afuwar nasu ne bisa tanadin Sashe na 212 na Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Nijeriya na shekarar 1999 da aka yi wa kwaskwarima wanda ya bai wa Gwamnan ikon yafewa ko kuma ɗaure duk wani mai laifin da ya cancanci zaman gidan yari.

Kwamishinan ya umurce su da su kasance jakadu nagari a cikin al’ummarsu tare da yi musu gargaɗin kada su sake aikata wani laifi.

Ya kuma yi nuni da cewa, gwamnatin jihar ta bayar da N20,000 ga kowannensu domin a sada su da ‘yan uwansu.

A yayin da yake zantawa da manema labarai, ɗaya daga cikin fursunonin da aka yi wa afuwa, Abdullahi Nasiru na garin Magamin Maitarko wanda aka yanke wa hukuncin kisa, aka kuma tsare shi a gidan yari na tsawon shekaru 18, ya yaba wa gwamnan jihar Zamfara kan yadda ya tausaya musu.

Ya yi alƙawarin zama nagari tare da mara wa dukkan manufofin gwamnati da shirye-shiryenta na cigaban jihar baya.