Majalisar Wakilai ta caccaki ASUU kan batun biyan albashin watannin da su ka kwashe a gida

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Majalisar Wakilai ta Tarayya ta caccaki Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i na Nijeriya ASUU, Farfesa Emmanuel Osodeke, bisa zargin shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, da yaudarar malaman jami’o’in kan janye yajin aikin da suka shafe watanni takwas suna yi.

Shugaban kwamitin yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na majalisar, Benjamin Kalu, a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, ya kuma bayyana cewa babu wani lokaci da Gbajabiamila ya amince da ASUU cewa za a biya malaman makaranta albashin tsawon lokacin da suka kwashe ba tare da shiga aji ba.

A cikin sanarwar mai taken ‘Martanin Majalisar Wakilai kan zargin da Osodeke ya yi wa Shugaban Majalisa’, Kalu ya yi nuni da cewa bisa ƙa’ida Gwamnatin Tarayya ta hana biyan albashin jami’o’i alhalin ba su yi aiki ba.

ASUU ta fara yajin aikin sai baba-ta-gani a ranar 14 ga watan Fabrairun 2022.

Gbajabiamila ne ya jagoranci shiga tsakani a rikicin da ya ɓarke tsakanin gwamnati da malamai, wanda ya kai ga janye yajin aikin a watan Oktoba.

Sai dai majalisar na zargin wasu ikirari da Shugaban ASUU ya yi a hirarsa da manema labarai a kwanakin baya.

Sanarwar ta qara da cewa, “A ranar Talata, 27 ga watan Disamba, 2022, Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i, Farfesa Emmanuel Osodeke, ya yi wata hira, inda ya zargi kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, da yin amfani da yaudara wajen shawo kan ƙungiyar don janye yajin aikin.

Ya kuma yi zargin cewa shugaban majalisar ya gaza cika rubutaccen alƙawarinsa na cewa gwamnati ba tare da ɓata lokaci ba, za ta biya bashin albashin ‘ya’yan ƙungiyar na tsawon lokacin da suke yajin aiki.

“A iya sanina, ko kaɗan shugaban majalisar wakilai bai yi alƙawarin biyan basussukan albashin da ‘yan ƙungiyar suke bi na tsawon lokacin da suke yajin aiki ba.

Majalisar wakilai ta taimaka wajen warware yajin aikin ta hanyar ɗaukar alqawurran inganta tsarin jin daɗin malaman jami’o’i da farfaɗo da kuɗaɗen don inganta ababen more rayuwa da ayyukan jami’o’in tarayya.

“Waɗannan alqawurra sun bayyana a cikin ƙudirin kasafin kuɗi na 2023, wanda ya haɗa da Naira 170,000,000,000.00 don samar da wani mataki na ƙarin girma a cikin ƙunshin jin daɗin malaman jami’o’i da ƙarin Naira 300,000,000,000.00 na kuɗaɗen farfaɗo da tattalin arziki.

“Bugu da qari, Majalisar Wakilai na ci gaba da yin aiki tare da masu ruwa da tsaki da Akanta Janar na Tarayya da Ƙungiyar Ma’aikatan Jami’o’in don sauƙaƙe ɗaukar abubuwan da Jami’ar ta fahimci da magance ba da lamuni a cikin tsarin IPPIS. Shugaban kwamitin kula da manyan makarantu na majalisar wakilai Aminu Suleiman ne ke kula da wannan yunƙurin.

“Farfesa Emmanuel Osodeke ya san cewa Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ba ta da wani haƙƙi na biyan malaman jami’o’i albashi na tsawon lokacin da suke yajin aiki. Wannan lamari ne da aka sasanta a cikin doka. Sashe43 (1) (a) Dokar rikicin kasuwanci, Cap T8, Dokokin Tarayyar Nijeriya (LFN).”

Kakakin majalisar ya bayyana cewa, muradin al’umma na ganin an samar da ɓangaren ilimi na manyan makarantu abu ne mai matuƙar muhimmanci ga duk wanda ya fahimci canjin ilimi a kowace al’umma.

Ya jaddada cewa a saboda haka ne majalisar ta tsaya tsayin daka wajen lalubo hanyoyin yin garambawul da inganta tsarin ilimin al’umma a ƙasar nan tun daga matakin firamare har zuwa manyan makarantu.

“Manufofinmu game da wannan ba za su cimma ba yayin da masu ruwa da tsaki suka zaɓi yin watsi da muhimman batutuwa da kuma yin la’akari da ra’ayoyi masu ƙarfi don goyon bayan ƙarya da farfagandar,” inji shi.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “hanyar rashin imani da Farfesa Osodeke ke bi wajen yin shawarwari da kuma alaƙarsa da ɓatagari a siyasance, manyan dalilan da suka sa jami’o’in ke yajin aiki na tsawon lokaci. Ayyukan sa na ci gaba da yin barazana ga ci gaban da ake samu don hana yiwuwar ci gaba da kawo cikas ga kalandar ilimi na jami’o’in.

“Saboda haka, ina kira gare shi, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar malaman jami’o’i, da ya daina yin kalaman ɓatanci ga majalisar wakilai da Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.