Kada ku ci amanar mu, Matawalle ga al’ummar Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Gwamnan Jihar Zamfara Hon. Bello Mohammed Matawalle ya yi kira ga al’ummar jihar da ka da su ci amanar shi a zave mai zuwa.

Gwamnan wanda yake neman kujerar shugabancin jihar karo na biyu ƙarƙashin inuwar Jam’iyyar APC, ya yi kiran ne a lokacin gangamin yaƙin neman zaɓen shi a garin Burdugau Shelkwatar ƙaramar hukumar Bungudu a jiya Alhamis.

Matawalle ya ƙara da cewa zai kawo ingantaccen sauyi mai maana idan aka zaɓe shi karo na biyu a matsayin gwamnan jihar.

“Ina kira ga al’ummar Jihar Zamfara musamman masu zaɓe da ka da su ci amanar mu wajen zaɓe domin samun gwamnati mai ɗorewa don samar da ababen more rayuwa gare su.”

Ya yi kira ga al’ummar jihar musamman masu zaɓe da su kauce wa duk wani nau’in nuna masu abin duniya daga wasu gurvatattun ‘yan siyasa don sauya masu ra’ayi wajen zave tare da tabbatar da sun zaɓe shi don ceto jihar daga durƙushewa musamman matsalar tsaro.

Haka zalika Matawalle ya nuna farin cinkin shi bisa yadda magoya bayan shi suka taru don nuna goyon bayansu gare shi a ƙaramar hukumar Bungudu lokacin yaƙin neman zaɓen shi.

Ya yi alƙawarin ci gaba da samar da ababen more rayuwa ga al’ummar jihar musamman mutanen yankunan karkara da birane a duk faɗin jihar idan aka zaɓe shi karo na biyu a lokacin zave mai zuwa.